Saturday, 29 December 2018

Yadda Ake Daina Kallon FinaFinan Batsa (Blue Film)

daina kallon fim na batsa

Kallon finafinn batsa bashi da kyau a rayuwar mu ko kaɗan sannan ma addinin musulunci yayi mana gargaɗi game da kallon tsiraicin wani. Saboda haka, yana da kyau mu daina wannan mummunar ɗabi'ar. Amma matsalar itace duk wanda ya saba kallon irin waɗannan finafinan zai sami matuƙar wahalar dainawa. Saboda haka idan kana son daina wannan halayyar akwai hanyoyi da yawa da zaka bi.

1. Ka sa a ranka cewa babu kyau. Tun kafin ka fara goge duk fianafinan batsa dake cikin wayarka ko komputa, ko kafin ka sanar da matarka/mijinki, aboki, wani dattijon arziƙi a unguwarku, cewa kana son daina wannan mummunar ɗabi'ar. Yanzu da duniya taci gaba ma akwai wasu shafukan yanar gizo-gizo wanda suke taimakawa mutane dake son daina wannan ɗabi'ar. Samun wanda zai ƙarfafeka a wannan yanayin zai taimaka sosai wajen daina wasa da gaba, da kuma kallon finafinan.

2. Ka ƙona duk CD/tarkardun batsa. Matuƙar kana ajiye da irin waɗannan takardun ko CD na batsa, to daina kallonsu zai yi maka wahala sosai. Saboda haka, ka ƙona su sannan kuma a goge wanda yake cikin komputa ko waya da duk wani abu daya danganci batsa.

3. Ka saka applikashan da zai katange shafukan batsa. Ko kana amafani da waya ko kumputa duk akwai applictation da ake kira da 'anti-porn'. Shi wannan applikashan ɗdin zai hanaka shiga duk wani shafi a yanar gizo da yake da abubuwan batsa. Amma fa idan zaka saka masa lambar tsaro wato password, yana da kyau ka kira wani ya saka lambobin da baka sani ba, domin kuwa idan kaji kano son kallo babu yadda zaka buɗe ba tare da wanna lambar tsaron ba.  Wasu daga cikin waɗannan applikashan ɗin sun haɗa da: Qustodio, Microsoft family Safety, Norton Family Online, Covenant Eyes da sauransu.

4. Yanke serbis na yanar gizo-gizo. Idan kaji kana son kallon waɗannan finafinan a yanar gizo to abu mafi sauƙi shine ka kashe data ɗin wayarka ma gaba ɗaya ko na komputa. Idan ma da hali ka kashe wayar ka ajiye ta.

5. Kashe lokaci da wasu abubuwan. idan ka saba zama haka kawai abu wani abinda kake yi, to lallai shaiɗan zai dinga raya maka ka kalli wannan finafinan musamman idan kai kaɗai ne a cikin ɗaki. Saboda haka ka sami abinda zai dinga kashe maka lokaci. Misali:
- ka fara motsa jiki: saboda motsa jiki yana bada wasu sinadarai a jikin mutum da suke sawa yaji daɗi.
- ka ɗan yi balaguro. Idan kana da halin barin unguwar da kake zaka iya tafiya wata unguwar na wani ɗan lokaci. Chanza waje zai taimaka sosai
Chanza ɗabi’u

6. Ka gane abubuwan da suke jawo maka kallon. Zaka iya samun littafin da zaka dinga rubuta abu buwan da suka jawo maka kallon fim ɗin batsa duk lokacin daka kalla. Zama ka iya rubuta abinda ya faru a lokacin. Misali abokanai dake zancen batsa, rashin bacci, shiga instagram, gajiya da sauransu.

7. Ka nemi aikin yi. Bincike ya nuna cewa idan mutum bashi da aikin yi suna iya fadawa cikin neam abubuwan kala-kala a cikin yanar gizo. Daya daga ciki shine fara kallon hotuna/finafinan batsa. Saboda haka ka nemi aikin yi da zai kashe maka lokaci. Zaku yarda dani idan nace mutumin dayake son aikinsa zai dinga yin aikin ne har a lokacin dana hutu ne, kenan bazai ma dinga tinanin kallace-kallacen batsa ba.

8. Ka nemi hanyar katange abubuwan dake jawo maka. Idan da hali ka katange abubuwan dake jawo maka kallon duk gaba ɗaya, amma idan bazai yiwu ba, sai ka fara kaɗan-kaɗan. Misali, idan kallon talla ne a TV yake taso maka da sha'awar kallon, sainka guji kallon TV a lokacin dakasan za'a saka irin waɗannan tallukan. Idan kuma babu yadda za'ayi ka guje wa abubuwan dake taso maka da sha'awar, to sai ka guje su a kwakwalwarka. Misali sai ka dinga hango kanka cewa gasu sunzo maka kuma gashi ka guje musu ta hanyar tinanin wani abun kamar abinci, tattaki da sauransu.

9. Ka shiga cikin mutane. Kowa ya sani kallon fim din batsa ba abinyi bane a cikin mutane, amma idan baka yarda ba zaka iya gwada kalla wanda nasan mutum bazai iya ba. Saboda haka, ka kasance cikin jamaa.

10. Ka nemi taimakon masana. Idan daina kallon fim ɗin batsa ya zama wahala a rayuwaka, ko kuma yana jawo maka wasu matsalolin, yana da kyau ka nemi malaman addini ko kuma malaman zamantakewa domin su taimaka maka.

11.Ka nemi waya mara abubuwa da yawa. Yawancin mutane da suke kallon wadannan fina-finan suna yinsu ne a cikin wayarsu babba. Saboda haka, idan kana son ka daina sai ka dauki matakin rabuwa da wayar hannunka domin ka nemo karama ko kuma wadda bazakaji dadin kallon ba a ciki.

12. Kayi aure. Idan rashin aure ne yake jawo maka kallon finafinan batsa, to abu mafi sauƙi shine kayi aure nan take. Idan kuma halin auren ne baka dashi to yana da kyau ka nemi malaman addini domin suyi maka bayani akan haramcin kallon finafinan batsa da kuma hanyoyin da ake bi domin a rage sha'awa da tayi ƙarfi sosai.
A takaice a lura da wadannan abubuwan:
- Ka sa a ranka cewa babu kyau.
- Ka sa a ranka cewa babu kyau.
- Ka saka applikashan da zai katange shafukan batsa.
- Yanke serbis na yanar gizo-gizo.
- Kashe lokaci da wasu abubuwan.
- Ka gane abubuwan da suke jawo maka kallon.
- Ka nemi hanyar katange abubuwan dake jawo maka.
- Ka nemi taimakon masana.
- Ka nemi aikin yi.
- Ka shiga cikin mutane.
- Ka nemi waya mara abubuwa da yawa.
- Kayi aure.

No comments:

Post a Comment