Friday, 28 December 2018

Yadda Ake Adana Madarar Nono Domin Jariri Har Zuwa Shekara Daya

adana madarar nono

Idan kin kasance mai shayarda jiriri, wataƙila zaki so kisan yadda ake ajiye madarar nononki ta daɗe batare da ta lalace ba domin a shayar da yaronki koda bakya nan. Ko kuma kina da madara da yawa a cikin nononki saboda haka kina son ragewa ba tare da ta lalace ba. Domin fahimtar abubuwan dana ambata a sama sai a karanta wannan rubutun.
1. A tatso madarar a cikin roba ko kwalba.  ya danganta da yadda kike son tatso madarar, wasu matan sunfi son amfani da injin zuƙowa, wasu kuma suna amfani da hannu. Kodai wacce hanya kika yi amfani da, yana da kyau ki wanke hannunki da ruwa da sabulu kafin ki fara. Sai ki samu waje ki zauna domin ki samu sukuni sosai.

2. A raba madarar a kwalabe da yawa.  domin a guji asarar madarar sai a raba a kwalabe ko robobi da yawa domin a saka a frigde mai ƙanƙara. Sai ki fahimci yawan madarar da yaronki yake buƙata a duk lokaci ɗaya domin ki zuba a kowacce kwalba. Ki lura kar a cika kwalba har zuwa bakinta, domin kuwa madarar nono tana kumbura idan tana zama kankara. Sannan kuma yaro yana ƙara girma, kina ƙara yawan madarar da kike ajiyewa domin ya ƙoshi.

3. A saka kwanan wata akan kowacce kwalba. Ayi amfani da marker da bata gogewa domin rubuta kwanan wata akan kowacce kwalba. Yana da kyau ayi amfani da madarar data daɗe kafin sabuwa. Yana da kyau a nemi hanyar banbance madarar yaronki idan kina kaishi gidan raino, domin gudin kar a bashi madarar wani yaron.

4. A ajiye a chan cikin freezer ɗin. kowa ya sani cewa chan cikin freezer yafi zama da sanyi idan aka hada shi da kusa da ƙofa. Hakan yana faruwa ne yawancin lokuta saboda buɗe ƙofar freezer ɗin da akeyi.

5. Ayi amfani da madarar cikin watanni shida zuwa shabiyu. Madarar nono zata iya zama a matsayin ƙanƙara har zuwa shekara 1. Amma akwai vitamin C ackin nono wanda yake lalacewa idan aka ajiye zuwa lokaci mai tsawo. Saboda haka zaifi kyau idan akayi amfani da madarar cikin watanni shida.

6. A narkar da tsohuwar madar a kafin sabuwa. Idan kin rubuta kwanan wata a jikin kwalaben zai yi miki sau'ƙi wajen gane tsohuwar madara. Yana da kyau kiyi amfani da madarar da tafi kowacce daɗewa ko kuma a zubar da ita.

7. A ciro madarar daga gidan ƙanƙara a saka a inda baya. Idan zakiyi amfani da madarar da gobe, sai ki cire ta daga gidan ƙanƙara tin da dare domin ta narke a cikin gidan da baya ƙanƙara. Kar a cire madarar gaba ɗaya daga cikin fridge domin ta narke, hakan zai jawo kwayoyin cuta su girma a ciki.

8. Idan yanzu ake so ta narke sai ayi amfani da ruwan dumi. Akwai lokutan da kike buƙatar madarar da wuri, saboda haka sai ki saka ta a cikin ruwan ɗumi bana zafi  domin ta narke.
9. A zubar madarar bayan awanni 24. Bayan kin narkar madarar to a ajiye ta a cikin fridge (ba gidan ƙanƙara ba) zuwa awanni 24 kawai. Sannan kuma a zubar da madara Idan aka cire daga fridge bayan awa 1 zuwa biyu. Sannan kar a ƙara mayar da ita gidan ƙanƙara bayan ta narke.

No comments:

Post a Comment