Monday, 31 December 2018

Hukuncin Kallon Hotuna Ko Fim din Batsa (Blue Film) A Musulunci


Bismillahir-rahmanir-raheem.

Allah madaukakin sarki yana fada a cikin littafi me girma cewa :  Kace: "Abin sani kawai, Ubangijina ya hana abubuwan alfasha: abin da ya bayyana daga gare su da 
abinda ya boyu,... ”  (Q. 7:33)

Kafin mu san komi, ya kamata mu fara sanin mecece al-fahsha?

Alfahsha ta danganci duk wani rashin da'a da kuma halaye wadanda suke bana kwarai ba, da kuma dukkan nau'i na abin kunya. al-fahsha zata iya zama; neman maza, kallon fina-finan batsa, shigar banza wanda mata keyi domin janyo hankalin mazajen da ba nasu ba, zina da sauransu.

A cikin al-qurani me girma da hadisan manzon Allah S.A.W anyi amfani da kalmar al-fahsha a wurare da dama domin fadakar da duk wasu ma'abota tarayya da maza ko matan da ba nasu ba don nuna fitinar da take dauke da ita.

Daga cikin qololuwar al-fahsha Allah ya hada da wanda yake/take da aure ya/ta aikata zina (Quran 17:32), da kuma masu aikata madugo ko neman maza (Quran 7:80, 27:54). Sannan dukkan malamai sunyi ittafaqin cewa kallon fina finan batsa yana daga cikin abin da ake kira da al-fahsha.
Allah me girma da buwaya yana fada a cikin littafi me tsarki cewa " lalle Allah na yin umarni da Adalci da kyautatawa, da bai wa ma'abota zumunta, kuma yana hani ga alfahsha da abinda aka qi da rarrabe jama'a. Yana yi muku gargadi, dammanin ku, kuna tunawa". (Quran 16:90)

Abinda zamu lura a wannan ayar shine, fadin Allah cewa yayi hani ga abin qi, ma'ana duk wani abunda duniya ta yadda bashi da kyau, mutanan ko wanne al'adu da addinai sun yi ittfaqin cewa wannan abun ba mai kyau bane to Allah S. W. A yayi hani akan wannan abu. Idan muka duba zamuga cewa gaba daya duniya sun kyamaci kallon fina-finan batsa a ko wanne irin shekaru.

Ga Al'ummar da basu da qarfin hana irin wannan mummunan aiki, se suke tilasta hana yin sa a fili, da kuma haramta shi a dukkan wani gidan jaridu, talabijin da sauran kafafan yada labarai, wannan ya ishe mu wa'azi da nuna cewa ba halin kwarai bane. Domin duk abinda zaka buya domin kayi shi, saboda kasan cewa duk wanda ya ganka, girmanka da mutuncinka zai zuba, kai kasan wannan abin ba abin arziqi bane, kuma haqeeqa Allah S. W. A yayi tir da Allah wadarai da irin wannan aikin da masu aikata shi.

Abin lura na biyu a wannan ayar shine Allah S. W. A a gaba ya qara yin wani hanin akan rarrabe jama'a wato ainahin shiga hurumin jama'a ko kuma shiga hurumin wasu, ma'ana wato wuce gona da iri akan wani abu, haqeeqa munsan cewa Allah baya son wuce gona da iri a cikin addini, abin fahimtar shine, duk wani shishshigi da wuce gona da iri ga mutane, ko Allah kansa, to Allah ya hane mu ga yin irin wannan aiki, ya 'yan uwa sanin kanmu ne cewa kallon fina-finan batsa wuce gona da iri ne ga iyakokin da ubangiji ta'ala ya shimfada mana, wanda tsallakesu kan kai mutun zuwa ga halaka bayyananniya.

Allah S. W. A ya hada shirka, kisan musulmi ba tare da haqqi ba da kallon tsiraicin mutane don a nuna mana cewa yana daya daga cikin manya manya laifuffukan da Allah baya so.

Mu sani ya yan'uwa musulmi, manzon Allah S. A. W ya fada mini cikin hadisi ingantacce cewa: Dukkanninku masu kiwo ne, kuma dukkan ku ababan tambayane game da kiwo da aka bashi. "

Kar mu manta da cewa se Allah ya tambayemu game da samartakarmu da loqacinmu yaya akayi muka gudanar dasu?Shin munyi abinda ya kamata ko kuma sabanin hakan?

Manyan malamai da dama sunyi maganganu akan kallon tsiraicin mutane.  Salman ya ruwaito a cikin Almabsud kitabul istehsan: Na gwammace in fado daga qololuwar sammai in dagargaje, da in kalli tsiraicin wani, ko in bari wani ya kalli tsiraicina.

Babban malami Sheik Muhammad Nur Abdullah yace: idan ka kalli wani wanda yake zina, ko a fina-finan batsa ko a hoto ko kuma ka kalla a fili,  duka haramun ne.

A qarshe mu tina abinda ubangijin mu me girma da daukaka yana fada cewa: " kuma kada kabi abinda baka da ilimi game da shi. Lalle ne ji da gani da zuciya, dukkan wadancan, (mutun)  ya kasance daga gare shi wanda ake tambaya. ". 

ya 'yan uwana mu sani cewa shaidan maqiyinmu ne, kuma zai yi iya bakin qoqarinsa wajen yaga cewa ya kaimu ga halaka da tabewa.

Allah ya karemu daga Sharrin shaidan la'ananne kuma jefeffe, yasa mufi qarfin zuciyarmu, ya gafarta mana zunubanmu baki daya.

Ameen.

By Auwal Idris Shanono

1 comment: