Tuesday, 11 December 2018

Yadda Doya Take Da Amfani A Jikin Mutum


HAWAN JINI DA CIWON ZUCIYA

Kamar yadda muka nuna a jadawalin baya cewa doya tana ɗauke da vitimin B6, mai yawa a cikin ta wanda shike taimakawa wajen gurɓata wata guba mai suna Homocyteine. Idan wannan guba tayi yawa a jini tana yin illa ga bututun da jinin yake bi, masu hawan jini da ciwon zuciya suna da yawan shi homocyteine a jininsu. Doya tana da pottasium da magnesium sune idan sukai ƙaranci a kan kamu da hawan jini. Mai hawan jini da ciwon zuciya zai iya amfani da doyar da aka gasa saboda tafi dafaffiya ko soyayya. Kuma ita ce magani. Mai wannan cuta zai iya yawaita cin doya don amfana da vitamin B6, da ake samu a cikin doyar.
BASIR (PILE)
Doya na dauke da fibre mai rigakafin basir amman idan ana son inganta amfanin doya wajen cutar sai a cita da ganye kamar latas, kebeji, alayyahu da zogale. Ana so a gasa doya idan za'a ci, domin tafi dafaffiya kuma ita ke magani.

CIWON SUGA (Diabetes)
Wajen ciwon suga doya na da fibre mai daidaita sugar da ke shiga cikin jini sannan tana da "magnesium" da "manganese" masu taimakawa jiki wajen amfani da suga. Cin doya yafi cin shinkafa 'yar waje domin mutum yana samun kariya daga cututtuka musamman wadda aka gasa.

RAGE ƘIBA (Slimming)
Idan mutum yana da ƙiba kuma yana so ya rage ta, to ya yawaita cin doya saboda sinadarin "fibre" kuma cin alkama, dawa, gero, zogale, acca da lansir suna da sunadarin "fibre" fiye da doya. Suma suna taimakawa sosai. Sannan kuma mai son rage ƙiba ya yawaita cin doyar da aka gasa.

TAIMAKAWA WAJEN SARRAFA ABINCI
Doya tana ɗauke da abinda ake kira da fibre wanda yake taimakawa wajen sarrafa abinci da ya shiga cikin hanjin mutum. Sannan bayan nan tana rage bayangida mai tauri. Saboda haka tana taimakawa wajen kar cikin mutum ya rikice.
TAIMKAWA KWAKWALWA
Doya tana da sinadarai masu taimakawa kwakwalwar ɗan Adam wajen gane karatu da saurin fahimtar abubuwa. Kamar yadda binciken masana ya nuna cewa mutanen da suka dinga cin doya har watanni shida sun sami karin fahimta sama da waɗanda basuci doya ba.

ƙARA SINADIRIN JINI
Jini yana da sinadarai da bature yake kira da RBC da kuma WBC. Shi wannan WBC shine yake ɗauke da sojojin jiki wanda suke faɗa da cuta idan ta shiga jikin mutum. Bayan nan kuma RBC shine yake sawa jini ya zama jar kala. Saboda haka, doya tana taimkawa jinin mutum.

ƙARA YAWAN GASHI
Gashi yana buƙatar sinadirin anthocyanins wanda yake ƙara masa tsayi da yawa. Ita kuma doya tana ɗauke da wannan sinadarin dama sauran wasu sinadaran irin Beta Carotene da Bitamin A. Idan gashi bashi da Beta carotene to zai yanƙwane ya kuma jawo dandruf.

KASHE CUTUTTUKA NA JIKI:
Doya tana da kashi 43 na Bitamin C wanda ake buƙata kullum. Bitamin C yana taimakawa jiki wajen yaƙar cututtuka da kuma abinda ake kira da free radicals.
RAGE HAƊARIN KAMUWA DA CUTAR JEJI
Kamar yadda na ambata a baya, doya tana ɗauke da abubuwa daban-daban. Doya tana ɗauke da sindaran dake yaɗi da free radicals wanda suke kashe haɗarurrukan dake jawo cutar jeji. 

RAHE HAƊIRIN HAIWUWAR BAKWAINI:
Bakwaini shine jaririn da ake haifa wanda bai cika watanni tara ba. Cin doya yana rage haiwuwar irin waɗannan jariran domin kuwa tana ɗauke da sinadarin Iron wanda mata masu ciki suke buƙata domin jariransu. Rashin wannan sinadirin shine yawanci yake jawowa a haifi jariri bakawaini. Saboda haka masana na bada shawarar a dinga cin doya.

FADAKARWA:
Haƙiƙa kamar yadda muka faɗa a baya game da cututtuka da magunguna waɗanda suke maganin waɗannan cututtuka watau na Asibiti ko waɗanda suke a cikin abincinmu da muke ci da yadda ya kamata mu yi amfani da ko dai nau'in abincin ko wasu tsirrai, domin kuwa mu gani yadda suka amfani wajen wasu cututtuka.

Allah (S.W.T) ya kawo cututtuka da kuma maganinsu saboda haka nake so in sanar da ku cewa akwai wani maganin mai ɗauke da sinadarai daban-daban a cikin sa masu matuƙar amfani wajen magance cututtuka daban-daban Insha – Allahu.
No comments:

Post a Comment