Thursday, 26 December 2019

yadda zaki saka saurayi ya so ki

 Idan kika lura da kyau zaki ga cewa a cikin samarinki akwai wanda yake sonki sosai amma baya son nuna yana son naki, to ta yaya zaki jawo hankalin sa yazo ya fada miki da kansa cewa yana sonki kamar ya mutu. Wannan abune mai sauqin gaske wanda baya buqatar wani dogon tinani.

1. ki dinga nuna masa kema biki damu dashi ba, loqacin da kika tabbatar cewa yana kallonki to ki nuna cewa bama ki san yana wurin ba.

2. ki yawaita kwalliyar da zata tashi hankalinsa, wanda zai futo da kyawunki, wanda idan ya ganki ko baiyi niyyar miki magana ba sai yayi, kina doso inda yake ki nemi wuri ki zauna tare da qawayanki ki dinga hira dasu kamar biki san Allah yayi halitta a wurin ba.

3. ki dinga kula wasu mazan a gabansa, yanda zai fahimci cewa bawai baki da masoya bane, amma kada ki yawaita kula mazan kar ya dauka cewa araha ne dake. kuma ba ko wanne irin maza zaki dinga kulawa ba, kar a samu matsala.

4. wani loqacin idan yana tare da abokansa, kije ku gaisa dasu amma shi karma ki kalle sa, hakan zai ja hankalinsa yaji me yasa shi kike mai hakan,ina tabbatar miki da kansa zai zo yayi miki magana.

5. ki dinga yawan yin yawo da abokinki namiji saboda hakan zai jawo hankalinsa domin ya kawo kansa.

No comments:

Post a Comment