Thursday, 26 December 2019

yadda za ka/ki gane wani/wata na son ki/ka

       Abune mai wahala ka gane cewa mutum yana son ka/ki, kuma zaka/ki ji kunya ka/ki tambayeshi, anan zamu fada muku wadanne hanyoyi ya kamata ka/ki bi domin ganewa ba tare da kin/ka tambayesu ba.

1. wasu idan suna sonka/ki za ka/ki ga yanda suke magana  in suna tare da kai/ke ya banbanta da yanda suke magana da wasu. yanayin yanda suke zama tare da kai/ke ya banbanta da yanda suke zama da ragowar mutane.

2. ka/ki dinga kula da yanayin yadda suke kallonka/ki. zaku lura cewa baza su iya hada ido da kai/ke ba kamar yadda suke yi da ragowar mutane.

3. ka/ki gane cewa a wasu loqutan soyayya kan shiga tsakanin abokai, idan kuka fahimci hakan, to ta/ya ce ya/ta na son ka/ki hakan bazai zama abin mamaki ba. sai ka/ki yadda ku more rayuwarku.

4. wasu mutanan kan nuna ma ka/ki soyayya ta hanyar janka/ki a jiki. misali, zasu iya cewa yayin da suke latsa wayarsu "kaga sabuwar waqar da nicky ta saka" ta/ya na nufin ka/ki matso domin ki/ka gani tare dasu, hakan na nuna cewa suna son su ji ka/ki a jikinsu, wanda hakan na nuna cewa ya/ta na son ka/ki.

5. idan duk ka/kika nuna musu wadannan abubuwa basu gane ba,abinda yafi sauqee shine ka/ki kira su ki/ka fada musu cewa ka/ki na sonsu. wannan ba wani abu a ciki. 

3 comments: