Thursday, 26 December 2019

yadda za ka/ki saka baban ki/ka farin ciki

 Shin ko kun san cewa saka iyaye farin ciki abu ne mai matuqar kyau? Ba abinda iyaye suka fi so kamar ‘ya’yansu su saka su farin ciki da jin dadin. To anan zamu fadi hanyoyin da zamu bi domin saka babanka/ki farin ciki.

1. Ya zamanto cewa loqaci bayan loqaci ka/ki na zuwa wurin baban kuna gaisawa, idan ya tambaye ka/ki cewa akwai wani abu ne sai ka/ki ce ba komai kawai dai ka/kin zo gaida shi ne, hakan zai saka yaji dadi sosai.

2. In ka/kika samu dama ki/ka dinga tambayar sa ya aiki? Da tambayoyin da zai fahimta cewa tabbas ka/kin damu dashi.

3. Kada ka/ki dinga gardama dashi idan ya fadi abu koda ka/kin san ba daidai bane, to ka/ki yi shuru a wurin, daga baya ka/kika fahimci cewa yana cikin farin ciki, yayin da kuke wata hirar za ka/ki iya dawomai da maganar ta salon hikima domin ka gyaa masa. Sannan idan yana ba ka/ki labarin wani abu, koda ba ka/ki son labarin, ka/ki nutsu ki/ka nuna labarin yana miki/maka dadi, idan abin dariya ne ka/ki yi, idan na jaje ne shima ka/ka nuna rashin jin dadin ka/ki.

4. Ka/ki dinga lura da abubuwa da yake so a dinga yi a gidan, sai ka/ki dinga yinsu kafin yace ayi, hakan zai saka masa farin ciki a zuciyarsa.

5. Ka/ki samu abokai na gari wanda idan ya gan ka/ki dasu zai zamo mai farin ciki a zuciyarsa.

6. Idan shi yake biyan kudin yanar gizo gizo da ka/kike amfani dashi to ya zaman to cewa ka/kin rage yawan amfani dashi domin ka/ki nuna masa tausayawa, hakan shima zai saka soyayyarka a zuciyarsa.

Ba wai munce iya wadannan abubuwanne zasu saka baban ka/ki farin ciki ba, se dai wadannan sune ginshiqai na saka shi farin cikin. 

No comments:

Post a Comment