Thursday, 26 December 2019

yadda ake sawa kowa ya so ka a dangi

  Shin kana son ace anfi sonka akan kowa a gidanku? Ko kuma so ace kowa na alfahari da kai a danginku? Na tabbatar duk wani da na kwarai yana so ace shine mafi soyuwa a danginsu sama da kowa. To abin tambayar shine ta yaya zaka cimma burin ka akan hakan? Wannan ba wani abu bane mai wahala sai dai yana buqatar jajurcewa da yin abinda ya kamata.

1. Da farko ya zama wajibi a kanka ka zamo mai tsari wajen gudanar da al’amuran rayuwar ka, ma’ana komai naka ya zamo yana da tsari da kamala.

2. Duk abinda kaga ya dace kayi, to kayi shi tin kafin ace kayi shi, misali kasan cewa za’a ce kayi aikin da aka baka a makaranta, to kafin ace ka dauko kayi, ya zamanto cewa kayi shi. Hakan zai saka a dinga maka kallon mai hankali kuma a dinga daukarka babban mutum.

3. Idan kayi laifi, ya zamanto cewa ka bada haquri da wuri, kuma ka yadda cewa kai kayi laifin, domin halin yarana da qananan mutane rashin amincewa da cewa sunyi kuskure.

4. Ya zama kana son ‘yan uwanka sosai, kana bawa yayyanka girman su, su kuma qannanka kana kyautata musu, hakan zai qara maka girma a idon manya da qananan yaran dake gidan.

5. Ka zamanto mai cika alqawari, idan kace zaka yi abu, ka tabbatar ka cika wannan alqawarin.

6. Kar ya zamo kana yawan musu da ‘yan uwanka domin hakan yana jawo raini, idan kaga abin zai wuce gona da iri sai ka ja bakin ka kayi shiru.

2 comments:

  1. After i obtained on your blog although placing interest merely slightly little bit submits. Enjoyable technique for long term, I'll be book-marking at any given time obtain types complete comes upward. Medicines in karachi

    ReplyDelete
  2. Ina naiman shawara gunka idan ka bani izini

    ReplyDelete