Friday, 27 December 2019

Yadda zaki saka mijinki farin ciki

 Mazaje da yawa suna qaro aure ne saboda matayansu basa musu abinda suke so, ko kuma ince basa musu abinda ya kamata suyi musu, wasu magidanta da muka tattauna dasu sunyi qorafi da yawa akan matansu, daga cikin bayanan wasu daga cikinsu suka ce maganar gaskiya rashin kula dasu ne yasa suka qaro aure. To abin tambayar shine, ta yaya mata zasu kauce wa irin wadannan matsalolin a gidajansu. Abu ne mai sauqi yin hakan sai dai sai kin sunkuyar da kanki kinyi abinda ya dace. Kadan daga cikin hanyoyin da zaki saka mijinki farin ciki sun hada da;

1. Abu na farko dai ya zama wajibi a gareki ki nuna masa cewa shi ne gaba da ke, ma’ana ki bashi girman sa, ki nuna mai cewa ba wanda kike girmamawa a duniyar nan sama dashi.

2. Ki goya masa baya dari bisa dari a duk abinda kika san nasara ne ga rayuwarsa, ki nuna mai cewa ai nasarar shi taki ce. Idan kina da hali ma ki taimaka masa da kudi da addu’a a duk loqacin da yake buqata, ki nuna masa kin fishi damuwa yayin da duk ya shiga wata matsala, sannan ki nuna kin fishi farin ciki duk loqacin daya samun nasara.

3. Ki dinga yawan tura masa saqonnin soyayya da nishadi yayin da yake kasuwa ko wurin aiki, domin hakan zai saka shi farin ciki ba kadan ba.

4. Ba ko wanne namiji bane yake tina ranar haihuwarsa yayin da ta zagayo, ko kuma ranar da aka daura muku aure da sauransu, ya zamanto cewa ko yaushe kina tina irin wadannan ranaku kuma kina basa kyauta idan ta zagayo.

5. Idan kika fahimci cewa mijinki mai yawan sha’awa ne to sai kiyi qoqari ki dinga biya masa buqatarsa akai akai ba sai kinga yana nema ba, ko baya buqata ke ki nuna masa cewa kina da buqata. Hakan zai saka shi yaji ko tinanin wata baya yi.

6. Abu mafi muhimmanci shine ki zamo mai so da yawan yin kwalliya, ki zamanto wacce bata da qazanta ko kadan. Domin maza basa son mai qazanta ko kadan koda shi qazamin ne.

7. Ki dinga mai girkin da yafi so, kuma in yazo kada ki barshi yaci da kansa, ki bashi da kanki.

8. Ki yawaita fada masa yadda kike sonsa, sannan ki dinga nuna masa a zahiri tabbas kina sonsa, kada ki bari ko kadan wata a can waje ta fiki nunawa mijinki soyayya, hakan ba qaramin hatsari bane ga rayuwar auranki.

9. In ya bata miki rai, kada ki hau shi da zage zage, ki bishi a hankali ki gaya masa. Hakan zai sa jikin sa yayi sanyi har ya gane kuskurensa. 

No comments:

Post a Comment