Friday, 27 December 2019

Yadda ake qara tsayi

  mutane da yawa suna son su qara tsayi amma abin ya gagara, yawancin mutane suna daina tsayi ne yayin da suka kai shekara 20 zuwa 25, to amma akwai hanyoyi wadanda idan kabi su to da ikon Allah tsayin ka zai qaru ba tare da gardama ba. karkade kunnuwan ka/ki domin jin wadannan abubuwa ba tare da ko sisin kobon ka ba.

1. shin abincin da ka/ki ke ci wanne iri ne, shin me gina jiki ne ko kuma bama kasan mai ka/ki ke ci ba. ma'ana, baka/ki san amfanin abinda ka/ki ke ci ba. To ka/ki saurara ka/ki ji, cin abincin dake gina jiki yana taimakawa kwarai matuqa wajan qara tsayin ka/ki. Abincin dake gina jiki sannnan su qara miki/maka tsayi sun hada da;
         a) ganye (salad, alaiyahu, yakuwa) da sauransu
         b) kwai, nama, kifi da sauransu
         c) lemo, kankana, abarba, dankali da sauransu

2. ka/ki yawaita cin kwai kullun, domin bincike ya nuna cewa yaran da suke cin kwai kullun sunfi yaran da basa ci saurin girma.

3. ka/ki yawaita cin abinci mai gina jiki, kamar madara, nama, kifi, zogale sosai. safe, rana da dare.

4. ka/ki dinga yawan cin abubuwan dake saka qarfin qashi, abinda bature yake kira da calcium containing food .

5. Ka/ki dinga yawan miqar da qashin bayin ka/ki kulum, hakan zai taimaka sosai wajan qara miki/maka tsayi.

No comments:

Post a Comment