Saturday, 28 December 2019

Yadda ake nade kyauta a kwali.

  Mutane da yawa suna son bada kyauta, kuma son su gyara kyautar da kansu, ma’ana su nannade ta, saboda wanda zasu bawa ya san cewa wahala suka sha, suka bata loqacin su domin yinta, don hakan ya qara musu wani kusanci da wancan din, ko kuma su nuna bajinta ko burgewa a wurin waccen, wanda yin hakan ba laifi ko kadan a cikinsa. Anan zamu koyar da yadda ake nade kyauta, ko yadda za ka/ki saka kyauta a kwali kafin ka/ki bayar da ita.

ABUBUWAN DA AKE BUQATA

A) Wrapping paper (takarda mai kyalli-kyalli)
B) Farin salatif
C) kwali

1. Da farko za ka/ki samo kwalin ka/ki mai dan girma wadda kyautar zata shiga ciki, ko ka/ki auna tsawon kyautar da yawan ta sannan se ka/ki auna girman kwalin sai ka/ki yanka shi, amma kwalin yafi kyautar girma.

2. Sai ka/ki samo abinda ake cewa wrapping paper (wata takarda mai kyalli da ake nade kyauta da ita) mai girma wacce zata dauki kyautukan duka. Idan ka/kika so za ka/ki iya nade su duka a hade, ko kuma kowanne daban-daban tinda qarshe dai duk cikin kwali za’a hade su.

3. Za ka/ki dauko wrapping paper din ka/ki, ka/ki shimfida shi shi a qasa, ta inda bangaran kyal-kyalin yana qasa sai ka/ki saka kyautar a kai. Sai ka/ki nannadeshi.

4. Kafin ka/ki nannade shi ka/ki tabbatar da cewa kyautar ta matse sosai a jikin wrapping paper din, sannan sai ka/ki juya ta yadda take a matsen ka/ki dakko farin salatif din ka/ki da ka/kika yanka ki/ka manna a jiki ta bayan, ta inda ya tattare kenan saboda matse shin da ka/kika yi.

5. Za ka/ki matse shine ta yadda takardar zata hadu a tsakiya, sannan sai ka/ki qara wani salatif din a kai saboda ya zauna sosai, idan ka/kin gama sai ki saka kwali, shima kwalin za ka/ki nade shi da wannan takardar mai kyalli, ta yadda zata bi jikin kwalin kamar tare akayi su. Sannan sai rufe shi da salatif.

Idan ka/kika kaiwa wanda ka/kika yiwa sai yaga kamar daga kamfani aka kawo masa/mata shi.

2 comments: