Friday, 27 December 2019

Yadda ake korar abokinka ko dan-uwanka daga gidanka

  Abokinka ko dan uwanka kan iya shiga matsala ta gida, kuma ya nemi taimakonka, baka da dalilin da yasa bazaka taimaka masa ba matuqar zaka iya. A inda matsalar take shine, yayin da ka taimaka masa ka dakko shi ka kawo shi gidanka, ya dan yi wasu kwanaki sannan ya samu nasa ya koma. Wasu da yawa basa komawa nasun, sai su zauna kamar gidan tare kuka siye shi. Kuma irin wadannan suna da wahalar kora daga gidan naka. Ta wacce hanya ne zaka iya korarsu? Wannan shine abinda zamu fada anan.

1. Ka fara gano dalilin da yasa baka son zama dasu, yadda zaka samu hujjar fada musu yayin daka tashi korar su. Misali, zaka iya cewa “ munyi magana dakai cewa wata uku zaka yi, amma yau shekara guda kenan, ya kamata gaskiya ka samo naka gidan ka koma” ko wani abu makamacin hakan.

2. Idan zaka mai magana, ka mai magana da tattausan lafazi, yanda zai fahimci cewa akwai matsala ne shi yasa kake so ya tashi. Kada kayi mai masifa, don hakan kai iya jawo rushewar zumuncin ku.

3. Kayi qoqarin bashi wuraren da zai iya komawa, hakan zai nuna mai cewa ai ka damu dashi, tinda har wurin da zai koma ma ka bincika masa.

4. Ka nuna masa cewa da gaske kake ba wasa ba akan lamarin, domin yayi gaggawar bar maka gida, saboda wasu basu san kara ba, sai ka nuna musu d gaske kake.

5. Duk hanyar da kake tinanin cewa in kabi bazai ji haushi ba, ka bi ta. Kuma kada kayi tinanin bazai ji haushin ba, kawai dai kayi kanka tsaye ba tare da jin tsoron komi ba.

6. Idan duk wadannan abubuwa busu yiwu ba, sai ka bashi qayyadajjen loqacin da zai tashi (notice) na sati biyu. Idan yaqi tashi duk da haka sai ka miqa shi ga kotu domin ta raba ku, ta koreshi, tinda bai san mutunci ba.

No comments:

Post a Comment