Sunday, 29 December 2019

yadda ake bambamce tsakanin mani, maziy da wadi.

 mutane da dama suna jin kunya ko nauyin su tambayi irin wadannan abubuwan ga malamai ko masana ilimi. abinda suke mantawa shine babu kunya a dangane da abinda ya shafi addininka. Domin Allah (SWA) yace " ka sanni kafin ka bauta min". To idan baka san addinin ka ba, taya zaka bauta wa ubangijin ka? 

Wasu zamu ga cewa basa banbancewa tsakanin maniyi, maziyyi ko wadiy. wanda hakan matsala ce babba wacce ta shafi tsarkin ka da kuma rayuwarka baki daya. Wadannan ruwaye guda uku da suke fita daga jikin dan adam dukkansu akwai hukuncin su daban, wanda sai kasan hakan ne zaka iya gane ta yaya zaka tsarkaka daga su.

**Maniyyi wani ruwa ne mai kauri da yake fita daga gaban mace ko namiji, wanda yake kalarsa fari ne ga maza kuma rawaya ga mata, yana fita ne da qarfi kuma loqacin jin dadi kuma fitarsa kan saka jikin mutum ya mutu hakan yake nuna qarshen jin dadin. ba lalle sai loqacin jin dadi yake fita ba ko da loqacin da mutum yaji baqar wahala ma yana fitar dashi. (fataawa al-lajnah al-daa'imah)

Fitar sa yana zama wajibi mutum yayi wankan janaba, wanda munyi bayanin yadda ake wankan janaba a rubuce rubucen da muka yi a baya.

**Mazhiy shima fari ne amma mara kauri, yana fita ne yayin da sha'awa ta taso ma mutum, ko dai loqutan da kake kallon wani abu na banza, ko kake tinanin wani abun banza, ko kana son kayi wani abun da ya danganci mata. Duka maza mata suna fitar dashi. Fitar dashi baya sawa ayi wanka, sai dai tsarki, yana karya alwala. Shi wannan ruwa ba mai kyau bane, fitarsa yana sawa ka/ki wanke inda ya taba sau uku, idan kuma ka/kika kasa gane inda ya taba sai ka/ki wanke tufafin baki daya sau daya. (fataawa al-lajnah al-daa'imah).

**Wadii kuma wani farin ruwa ne da yake futowa daga mafitsara, a qarshen fitsari, baya sakawa ayi wanka, sai dai yana karya alwala.

Wannan dan taqaitaccen bayani kenan akan maiyyi, maziyyi da wadiyyi. Da fatan zai zama alfanu ga masu neman sani.

1 comment: