Thursday, 26 December 2019

Yadda zaka/ki yi sabo da sabon abokinka/ki

      Sanin kanmu ne cewa sabo da mutum ba abu bane me sauqi,mutane da yawa basu san yadda zasu saba da sababbin abokansu ba, wani loqaci zamu ga cewa mun dade da mutum sosai amma bamuyi sabon da ya kamata muyi dasu ba. Zamu baku shawarwari tare da hanyoyin da indai kun bi su to babu shakka sai kun shaqu da wannan abokin naku ba tare da wata matsala ba.

1. Hanya ta farko ita ce; idan kuna hira dasu kafi maida hankali akan abinda ya shafe su, misali, mai suke da sha’awar yi a rayuwarsu, shin mene ra’ayinsu a hankar siyasar qasa, ko suna da masaniya akan me yake gudana a bangaran lafiya ko kuma bangaren ilimin al’umma, shin yana da budurwa/tana da saurayi. Daga irin wadannan tambayoyi zaka gane ina suka fi karkata,wacce hira suka fi so kayi musu.

2. Idan ka fahimci hanya ta farko to se kayi qoqarin dinga zuwa wurinsu a loqacin da kasan basa komai, ka dinga yawan yi musu wannan hirar ko labarin da kake ganin yafi son sa. Ita tabbatar maka da sannu da kansu zasu fara zuwa wurinka suna neman ka basu labarin akan wannan lamarin.

3. Kada ka sake koda wasa ka yawaita basu labarinka, a’ah kayi qoqari ka barsu su dinga fada maka abinda suke so su fada, koda baka jin dadin hirar, ka nuna cewa ai ka san wani abu daga ciki ko kuma kana fahimtar abinda suke fada, hakan yana saka mutane su dinga son su shaqu dakai domin kana basu loqacinka.


4. Wani loqacin ka dinga fada musu wani abinda su sun san cewa in ba wanda ka yadda dashi ba bazaka iya fadawa wannan ba, saboda sirrin ka ne sosai, ka nuna musu cewa saboda ka yadda dasu shi yasa kake fada musu hakan.

5. Ka nuna musu cewa suna da muhimmanci a rayuwarka, idan biki ko suna ko wani muhimmin taro ya tashi, ka dinga halatta domin nuna farin cikinka, haka zalika idan mutuwa ce kaje ka taya su baqin ciki hakan zai saka shaquwa da qauna tsakaninku.

Wadannan hanyoyi bashi kenan su ba, nan gaba zamu ci gaba da kawosu daki daki, na tabbatar zaku samu dacewa idan kukayi hakan.

No comments:

Post a Comment