Thursday, 26 December 2019

Yadda zaka yi soyayya da mutum biyu

     Shin ka taba shiga tsaka mai wuya akan kana son ‘yan mata guda biyu ko kuma kina son samari biyu? Yaya ka/kika yi a wannan yanayin? Shin ta wanye lafiya ko kuma kaci duka a qarshe? Duk wadannan tambayoyine da mutanan da suka tsinci kansu suna son mutane biyu suke yi. Duk wannan ba wani abun daga hankali bane. Sanin mune cewa Allah yayi mu jinsi biyu, to ba abin mamaki bane idan ka/kika tsinci kanki/ka a cikin irin wannan yanayin, abu mafi sauqi shine ka/ki zauna ki/ka nutsu ka karanta wadannan hanyoyin da zasu warware maka/ki matsalolinki/ka ba tare da wani bata loqaci ba.

1. Nasan zakuyi mamaki kuce ai wahala ne yin hakan, amma ba wata wahalar abin lura shine ka/ki bawa kowa haqqin sa/ta a loqacin daya dace. Ka/ki fadada tinaninki/ka domin kwakwalwar mutun tafi qarfin abubuwa da yawa.

2. Ga wasu, saurayinta/budurwarsa ba ya/ta masa/mata wani abun da yake/take so, wanda dayar tana masa, misali wataqila waccan bata ita hira ba, shi kuma mutum ne mai yawan son hirar duniya, ko kuma baya bata kulawa da dadadan kalaman soyayya da take so ga wancan shi kuma yana bata, hakan zai saka ko shi ko ita din ya/ta samo wanda yake/take masa irin abubuwan don jin dadin rayuwarsa. Amma zan bada shawara anan yana da kyau ka/ki fada wa dayan cewa akwai wanda/wacce ka/ki ke gani saboda dalili kaza da kaza.

3. Kar ki/ka manta cewa kai/ke kadai ce ka/ki ka san abin da yafi dacewa ga rayuwar ka/ki. Saboda haka kar wani yazo yana gaya miki/maka cewa ai wannan bai dace ba, tinda dai rayuwar kace ba rayuwar wani ba. Ka/ki yi tinanin jin dadin da yake cikin soyayya da mutane biyu, hakan zai taimaka maka/miki wajan qarfafa miki/maka gwiwa don ka/kiyi. Kamar yadda wata qawata ta taba fadamin cewa “ai gida bitu maganin gobara” ma’ana idan dayan ya qone sai ka koma dayan, to idan daya ya bata miki/maka rai sai ki/ka koma a farantama/miki acan.

4. Wasu suna ganin cewa ai indai kana buqatar zaman lafiya a rayuwarka shine kaso mutum daya. To amma ni fahimtata anan itace indai kai a kanka ka/ki ka ga cewa zaka/ki iya kula da guda biyun ba tare da matsala ba ki/ka manta da wani labarin mutuna ki/ka je abinda ka/ki ke ganin yafi dacewa da rayuwarki/ka.

5. Idan namiji ne kai zaka iya auran su duka biyun saboda wataqila dalilin da yasa kake son ko wacce daban, qila daya ta iya girke ne sosai, dayar kuma qila ta iya bada kalaman da masoya suke son ji kuma ta iya soyayyar zamani, ko kuma dayar ta iya kwalliya ita kuma dayar bata damu da kwalliya ba amma tafi dayar kirki da kyau qila. 
 --Idan mace ce ke kuma sai ki tsaya kiyi duban tsanaki kiga waye idan kika aureshi zaki ji dadi sosai, wayo zai nuna miki soyayya kamar ya hadiye ki, kuma kin san ba abinda zai sa ya rage wannan so da qaunar da yake nuna miki har abada, waye zai girmama ki sosai da ‘yan uwanki. Sai ki ajiye dayan ki so na gaskiyan ko da wancan yafi shi iya soyayya da dadadan kalamai. 

No comments:

Post a Comment