Thursday, 26 December 2019

Yadda zaka hadu da iyayen budurwarka

      Samari da yawa suna shiga damuwa duk loqacin da aka ce zasu je gaida surukansu, wanda kuma zuwan ya zama dole, ba na fada maka wadansu hanyoyi wadanda idan kabi su hankalinka kwance zaka je ka gaida su ka dawo kai kace ma ba ayi ba. Kada kayi tinanin zaka biya kudi, a’ah kyauta zaka same su ba tare da ko sisin kwabo ba.

Wadannan hanyoyi sune kamar haka;

1. Ka tabbatar ka saka manyan kaya, ma’ana kayi shigar kamala irin ta hausawa, sannan ka saka turare mai qamshi kuma ba mai qarfi ba, domin yanayin shigarka shi za’a kalle ka dashi.

2. Kaje da wuri, misali idan kace qarfe 2 na yamma zaka je to ka tabbatar kaje akan loqacin, domin hakan zai nuna cewa kai mutum ne mai cika alqawari.

3. Ka nuna kunya da kawaici a gabansu, koda ace kuna wasa sosai da buduwar taka to sai kadan rage kadan a gaban su.

4. Sannan ka tabbatar ka basu girman daya kamata ka basu, kada ka dinga hada ido dasu, koda sunce kaci abinci tare dasu kada kaci, kada ka fara miqa musu hannu ku gaisa sai dai inn su suka fara miqo maka.

5. In zakayi maganar rayuwarka, to ka tabbatar ka fadi gaskiya, kada kayi qarya wai don ka birge su.
x

No comments:

Post a Comment