Thursday, 26 December 2019

Yadda ake mutane ke rasa gidajansu

      mutane da dama suna rasa gidajansu ta hanyoyi da dama, wasu hanyoyin na larura ne wasu kuma na sakaci ne. Anan zamu tattauna akan dalilan da yasa mutane ke rasa gidajansu ko su koma gidan haya ko kuma su koma rayuwar qasan gada, wasu kuma ma su koma kwanan kan hanya.

1. Da yawa rashin aikin yi ne ke saka wa su rasa gidansu, ko su siyar ko kuma a kwace saboda bashin da suka ci suka kasa biya, musamman yanzu da rashin aikin yi ya qaru da kusan kaso 7 daga cikin 100, hakan ya saka yawan adadin mutanan da suka rasa gidanjansun sun qaru.

2. Matsalolin dangi: misali akwai rashin lafiyar da zata saka dole a sai an siyar da kadarorin dangin wanda ya hada harda gidan, wannan shima daya daga cikin manya manyan dalilan da suke sawa mutane su rasa gidajansu.

3. A wasu garuruwan siyan gidaje kanyi wahala matuqa kwarai, hakan yana sawa mutane basu iya siyan gida ko mallakar gida. Wannan yana sawa mutane su rasa gidan zama sai dai su koma gidan katako da sauransu.

4. Mafiya yawancin masu shaye-shaye wadanda shaye-shayen nasu yayi qarfi har yakai ga sun fara rasa hankalinsu da tinaninsu, suna daina kwana a gida saboda matsalar kwakwalwarsu data fara tabuwa, ko kuma wadanda ake haifa da matsalar kwakwalwa suma sukan bar gida su koma kwanan hanya ko daji.

Wadannan kadan daga cikin dalilan da yasa mutane ke rasa gidajansu kenan.

No comments:

Post a Comment