Thursday, 29 August 2019

Yadda zaka saka budurwar wani ta dawo sonka

    
 YADDA ZAKA SAKA BUDURWA WANI TA DAWO SONKA

A mafi yawancin loquta ana samu kaga cewa kana son yarinya ita kuma tana son wani, ko kuma bama ta san kana sonta ba. To tambayar ita ce tayaya zaka janyo hankalin yarinyar nan ta fara sonka in zai yiwu ma ta koma sonka kai daya. A mafi yawancin loquta da wuya kaga yarinya wacce bata da saurayi, kuma kai a zancan gaskiya bazaka iya rayuwa babu ita ba. Ka biyomu domin sanin hanyoyin da zaka bi domin shawo kanta ka fara sonka. 

1. Kar kayi tinanin canzawa daga yanayin rayuwar ka da kake ciki, wato ka fara tinanin dauko wata rayuwar ta qarya, eh, nasan kun fahimci me nake nufi, in kai me kudi ne ka futo mata a talaka ko kai talaka ne ka futo mata mai kudi. ka futo mata a yadda kake.

2. Kayi qoqari kasan yarinyar sosai, kamar abinda take so, me tafi yi, me take son yi, in tana aiki, wanne irin aiki take, in makaranta take me take karanta, abubuwa dai da dama a kanta.

3. Kayi qoqari ka san wasu daga cikin qawayenta, su fara zama qawayanka, daga nan ka dinga binsu in zasuyi hira ko cin abinci kuna zuwa tare, a nan zaku fara magana kaga ka dan fara samu dama.

4. Idan hakan bai yiwu ba ka tabbatar kun shaqu da aminiyarta, ina tabbatar da cewa ko waye a wurin indai aminiyartata ta amince maka, se anyi gaba dashi, ka shiga.

5. Kuma sannan maganar gaskiya se kayi haquri, bawai loqaci daya zata ajje saurayinta ta dinga bata hankalinka ba, se ka jure wasu abubuwan sosai, se ka rufe idonka. Haquri yana da matuqar muhimmanci a wannan lamari. 

6. Ya zamanto cewa kana fada mata irin abubuwan da take so in kun zauna kuna hira, ka zama mai yawan bada dariya, ta inda har qawayanta zasu dinga yawan yabonka, kuma dole ka zama mai yawan kyauta. Dan kaima dai kasan yarinya batta kwatuwa cikin sauqee. Kudi suna doka muhimmaiyar rawa matuqar gaske.

7. Ka kiyaye ina qara maimaitawa kar ka kuskura kace mata kana sonta alhalin buku dade da haduwa ba, kayi haquri, a hankali ka dinga nuna mata wasu alamomin da zata gane, har Allah yasa ta gane.

No comments:

Post a Comment