Thursday, 29 August 2019

Yadda zaka kula yarinya a cikin mutane

     Sanin duk wani mai mu’amala da mata ne cewa mata basu fi son a kulasu ba yayin da suke cikin mutane, matuqar bawai kun saba bane, ko kun saba se kayi haquri wani loqaci. To yanzu misali kaga yarinya kuma tayi maka, kuma kana tinanin in ka kyale ta ba lalle ka qara ganin ta ba, kuma tana cikin mutane, yaya zakayi?

1. Abu na farko da zaka fara yi shine, kayi qoqari kasan yadda zakayi ka shiga hirar da suke yi.

2. Idan ka samu ka shiga, kar ka fara magana har se ka fahimci hirar me sukeyi, in zai yiwu ka fara da abinda zai basu dariya.

3. Sannan kada ka bari hirar ta qare da wuri, kayi ta qirqiro abubuwa har se ka gano wanne irin labari yarinyar tafi so.

4. Amma in ka fahimci ranta ya baci ka haqura.

5. Ka fi yawan bada labari kana dan kallonta, hakan zai saka taji alamar akwai wani abu, to ko bayan nan kace mata kana son magana da ita ina gayama bazata yiwu tace maka a'ah ba. 

No comments:

Post a Comment