Thursday, 18 July 2019

Yadda ake gyaran gashi da ruwan shinkafa

Shin ko kin san cewa wanke gashinki da ruwan da aka wanke shinkafa yana qara abubuwa da dama? Domin ruwan da aka wanke shinkafa yana da sinadarai masu yawa wadanda suke qarawa gashi qarfi,tsayi kuma sannan ya qara masa kyau da haske. Zaki iya wanke gashin ki da ruwan shinkafa sau daya a sati, ko duk loqacin da kika yi shampoo, ko kuma loqqacin da kika wanke shinkafa. Zaki iya samun ruwan shinkafa a wurin wasu ko kuma ki hada da kanki. Yanda zaki samu ruwan shinkafa a gidanki shine:

1. Ki samo shinkafar ki me kyau, kofi daya (1), ko kuma duk yadda kike so ta zama.

2. Ki samu ruwa kofi 4 ko 5, ki zuba wa shinkafar, se ki barta ta jiqu na minti 15 zuwa 30.

3. Ki dinga yawan juya shinkafar yayin da kika jiqa ta domin kar ta dunqule.

4. Ruwan yana komawa kalar ruwan madara sannan kika ga kumfa na taso wa a sama, hakan na nuna cewa yayi yadda ake so.

5. Se ki juye ruwan a wani wurin, ma’ana ki raba shi da shinkafar.

6. Se ki jiqa gashin naki a cikin ruwan, in zai yiwu ki bashshi ya jiqu na kamar minti 20 zuwa 30.

7. Se ki wanke gashin naki da ruwan sanyi ki taje kan naki, har se kin tabbatar da duk wani abun shinkafar ya fita daga kanki. Sannan ki daure gashinki. Zaki ga abin mamaki idan kina yawan yin hakan.

8. Zaki iya saka shinkafar a wuta cikin ruwa har se ruwan ya tafasa, yana fara tafasa se ki sauke shi ki jira ya huce, sannan se ki bi wadancan hanyoyin da aka zayyana a baya.

No comments:

Post a Comment