Thursday, 18 July 2019

Yadda ake sawa dimple ya futo
Dimple wani abu ne da mata da yawa suke so, domin a ganinsu kyau yake qara musu, wanda kuma hakanne. 
Shin ko kina da sha’awar kema ki samu? Ko kina so kema ace kina da shi. To ga hanya mafi sauqi da in kika bita to tabbas zaki samu wannan dimple din da kika dade kina sha’awarsa.

1. Ki fara da horar da kumatunki wajan motse shi kamar kin sha tsamiya ko wani abu me tsami, ta yadda kumatunki zai zama ya shige ciki.


2. Ki yawaita yin murmushi, duk loqacin da zakiyi murmushin ki saka dan yatsan ki a dai-dai inda kike so dimple din ya futo miki, ya zamanto cewa kin bude bakinki sosai yayin yin murmushin.


3. Ki dinga lotsa wurin da kike so dimple din ya futo miki na sakan talatin (30) a kullun


4. Ki duba inda ya dan lotse a kumatunki, ki yawaita lotsa wannan wurin ko da yaushe.


5. Idan duk hakan bai yiwa ba, akwai mutanan da aikin su kenan a asibiti, wato su fitar maka da wannan dimple din, amma hakan yana da hatsari matuqa, domin kina iya kamuwa da wasu cututtukan na baki yayin yin hakan

No comments:

Post a Comment