Friday, 19 July 2019

Yadda ake saka kakanni farin ciki


Kakanni na taka muhimmiyar rawa a zamantakewar rayuwar hausawa, musammam ma ga jikokinsu, har tana iya kaiwa kaji ana kiran yaron da yake da shagwaba da fitina da cewa “goyon kaka” ne, saboda sangarta yaro da suke yi. Saboda haka ya kamata su  jikokin su samar da hanyar da zasu farantawa kakannin nasu rai. Anan zamu fadi hanyoyin da zaku bi domin ku farantawa kakannin naku rai.

1. Da farko ka san wanne irin abubuwan suke yi domin jin dadin kansu. Misali idan kakanka/ki ya/ta na son zuwa yawon shaqatawa gidan namun daji, ko gurin ruwa, to sai ka/ki dinga zuwa ka/ki na kaisu duk ranakun qarshen mako.

2. Mun san tsofaffi da son yin hira, yin hirar mutane da tarihin abinda ya wuce zai taimaka sosai wurin faranta musu rai

3. Ka/ki zabi rana guda da ko yaushe zaki/ka dinga ziyarar su, kuma ka/ki je akan loqaci da abubuwan da suke son ci ko sha.

4. Idan kuna tare kada ku dinga nuna kun qosa da hirar da suke muku, kuma ku basu hankalinku dari bisa dari, kada ku dinga raba hankalinku gida biyu.

5. Ku dinga tayasu gyaran gida, kamar su share share, goge goge da sauransu, hakan zai saka su farin ciki matuqar gaske.

6. Duk in zaka/ki yi wani taro na abinda ya shafi rayuwarka/ki, misali, tina ranar haihuwar ka/ki, zagayowar ranar bikin ka/ki da sauransu, ka/ki gayyace su domin taya ka/ki murnar wannan ranar, hakan zai saka su farin ciki sosai.

No comments:

Post a Comment