Monday, 20 May 2019

Yadda zakiyi soyayya da namiji mai aure

        
Wasu nasan za suyi mamaki, shin ta yaya mace zata so namijin da yake da aure. To amma duk wanda yasan rayuwar soyayya, to na tabbatar yasan cewa zuciya bata da qashi, kuma ba wanda yake zaban wanda yake fara so, sai dai kawai kiji kin fara.
To tambayar itace duk wacce tace tana son ta yi soyayya da namiji wanda yake da aure, se a tambayata shin kin shirya zama da shi komwanne irin yanayi ne? Na san zaku yadda dani “eh” zata ce in har tana son shi tsakani da Allah. To yaa ke ‘yar uwa, gyara zamanki domin sannan ki karkade kunnuwanki domin in baki wani sirri na soyayya da namiji mai aure:

1. Ya zama wajibi a gareki ki rufe kunnuwamki akan masu cece-kuce na qasar hausa akan soyayyar taku, ya zamanto cewa, duk wasu gutsiri tsoma da mutane keyi a kanki, kin yi uwar shegu da su.

2. Ko kin san cewa namiji mai aure yafi sanin darajar mace akan wanda bai taba yin aure ba, yasan darajar iyali, darajar ‘ya’ya da sauransu, kuma yawanci bazai miki wasa da zuciya ba kamar yadda saurayi zai miki.

3. Shawara gareki, dole ki danne kishin ki, saboda sai yafi bawa matarsa da ‘ya’yansa loqaci fiye da ke, ki nuna masa wannan dan loqacin da yake baki ba qaramin dadi kike ji ba, kada ki dinga nuna kishi mai zafi akan matarsa da yayansa.
4. Ki nuna masa cewa kin damu da iyalansa kamr yadda ya damu dasu, ki rinqa yawan tambayarsa ‘ya’yansa da sauransu in har hakan yana saka shi farin ciki, domin zai ga kin damu da abinda ya damu dashi

5. Sannan abu na karshe ki tina ba wanda ya isa ya hanaki son abinda kike so, domin rayuwarki ce bata kowa ba, indai har yana sonki kina sonshi, qauna ta yawaita a zuqatanku to ki ci gaba da abinda kike ba gudu babu jaa da baya. 

No comments:

Post a Comment