Monday, 20 May 2019

YADDA ZAKAYI/ZAKIYI QURUCIYA MAI BAN SHA’AWA

        


Burin ko wanne yaro ace ya girma ya zama wani abu zai taimakawa kansa da iyayensa hadi da yanuwansa a wani loqacin, to abin tambayar shine wacce hanyoyi zaka/ki bi domin cimma wannan manufar taka a rayuwa. Ga jerin gwanon wasu shawarwari da in dai ka dauke su, to da taimakon ubangijin mutane da aljanu sai ka samu nasara.

1. Ka/ki taimaka wajan taimakon al’umma musamman ma marasa qarfi,duk inda ka/ki ka san ana aikin taimakon mutane jeka/ki ka/ki sa hannu.

2. Ka/ki tabbatar ka/kina da wata manufa ta kwarai a rayuwa wacce ka/kike son cimmawa a rayuwa. Misali; ka/kina son zama likita, ko kuma a’ah na’ura mai kwakwalwa ka/kike son iya koya sosai da sauransu. Ka/ki tafi akan wannan abin har sai ka/kin cimmasa, ya zamanto cewa shi yake qarafafa maka gwiwa.

3. Kada ka/ki sake ace an taba ganinki/ka a wurin wani aikin da ba mai kyau bane, domin hakan zai lalata maka/ki quruciyar ka/ki.

4. Ya zamanto cewa ka/ki na jin maganar iyayen ka/ki, sannan da malaman ka/ki, domin hakan zai saka mutane su shedai ka/ki, kuma shaidar kwarai bata wasa ba.

5. Ko yaushe ka/ki rinqa tinawa, abokakinka/ki da ka/kike yawo dashi shi yake nuna waye kai/ke. Saboda haka ya zamo dole ka/ki dinga yawo da abokan kwarai.

6. Ka/ki zama mai dagewa da jajurcewa a makaranta, domin hakan zai taimaka sosai domin cimma abinda ka/kike so anan gaban.

No comments:

Post a Comment