Friday, 12 April 2019

Yadda ake mayar da hakora farare a cikin awa dayaKowa yana so hakoransa su koma farare musamman idan mai yawan murmushi ne. Zuwa wajen likitan hakori lokaci bayan lokaci zai taimakawa mutum wajen samun hakori mai haske. Amma akwai lokacin da kake so hakoran suyi haske saboda wani waje da zaka je. To, akwai abubuwan da zasu taimaka maka a wannan lokacin.A takaice

Zamu tattauna akan wadannan abubuwan
- Amfani da baking Soda.
- Amfani da hydrogen peroxide.
- Aci strawberry.
- A guji cin abincin da zai dafar da hakori.
- Amfani da man goge hakori mai saka haske.
- Amfani da Whitening strip.
- Amfani da whitening pen.
- Aje wajen likitan goge hakori.
- Amfani da injin laser.Hanya ta daya: amfani da abubuwan gida


1. Amfani da baking Soda. Idan aka samu baking soda zata taimaka wajen haskaka hakorin mutum a cikin mintuna kadan.
- A sami tawul ko tsumma mai kyau sai a goge hakoran da kuma ragowar yawu dake jikin su. A jika brush na goge baki sannan a tsoma shi a cikin baking Soda din. Sai a goge baki da ita kamar yadda aka saba yi kullum, a bawa hakoran 16 dake gaba muhimmanci. A goge bakin kamar na mintuna uku.
- A lura da cewa baking soda tana iya lalata dasashin hakora. Saboda haka kar a mayar da ita abin wanke baki kullum. Za’a iya amfani da ita kamar sau biyu a mako guda.

2. Amfani da hydrogen peroxide. Shima yana taimakawa wajen haskaka hakora kuma bashi da wata illa sosai, matukar ba hadiye shi akayi ba.
- hanya daya da za’a iya amfani dashi, shine a sami tusmma mai kyau a tsoma shi cikin ruwan sai a goge hakoran dashi.
- hanya ta biyu, itace a kuskure baki da cikin murfi na ruwan ko kuma a saka brush na goge baki a ciki sannan a goge baki dashi.

3. Aci strawberry. Bayan anci abinci, a dan sami strwaberry aci domin yana taimakawa wajen mayar da hakora farare. Idan babu strwaberry, za;’a iya samun apple, pear ko karas domin suma suna taimakawa sosai wajen haskaka hakora.

4. A guji cin abincin da zai dafar da hakori. Idan ana so hakora su zauna da hasken su, yana da kyau a guji cin abinci ko abin sha da zai sa hakoran su dafe. Misali kamar coffee, bakin shayi da sauransu.
- idan kuma kana san amfani da abubuwan dana ambata a sama, za’a iya sha ta hanyar amfani da abin zuka (staw) ko kuma a shafa vaseline kadan a saman hakoran.
- ko kuma a tauna chin gum mara suga bayan an gama shan wadannan abubuwan.Hanya ta biyu: amfani da kayan shago


5. Amfani da man goge hakori mai saka haske. Duk da cewa man gopge hakori ma saka haske baya aiki cikin awa daya, amma kuma zai taimaka wajen sawa hakorin ya kara walkiya.

6. Amfani da Whitening strip. Ana siyar dasu a shaguna da stores. Amma ana amfani da kamar strip guda biyu a cikin rana daya kuma sai an barshi kamar mintuna 30. idan za’a siya a duba abubuwan dake ciki idan anga akwai “chlorine dioxide” to kar ayi amfani dashi domin yana lalata dasahin hakori.
- bayan an siyo sai a bude a lika guda daya a hokran sama, daya kuma a hokoran kasa,  sanna a kyale su har zuwa mintuna 30.
- domin samun sakamako mai kyau yana da kyau a ci gaba da amfani dasu har zuwa kamar mako biyu.

7. Amfani da whitening pen. Shi kuma wannan ana yinsa ne kamar biro na rubutu. Amma kuma akwai man haskaka hokori a ciki.
- domin amfani dashi, a bude murfin sanna a juya kansa domin fito da man. Sai a tsaya a gaban madubi sannan ayi murmushi sosai sanna ayi amfani da biron wajen yiwa hakoran fenti.
- sai abar bakin a bude har sakannni kamar 30 domin man ya bushe. Ayi kokari kar aci/asha komai na mintuna kamar 45 bayan an saka man.
- domin samun sakamako mai kyau, yana da kyau a maimaita wannan sau daya a rana har na wata daya.Hanya ta uku: amfani da kayan asibiti


8. Aje wajen likitan goge hakori. Yana da kyau duk bayan watanni shida aje wajen likita domin wankin hakori.
- hakan zai taimaka wajen kare hakorinka daga duk wani abu mara kyau.

9. Amfani da injin laser. Shima wannan injin yana aiki sosai amma kuma yana da tsada sosai.
- za’a saka man goge hakori a jikin hakoran sannan a saka roba a saman hakorin. Daga nan kuma sai a haska laser din. Anayi kamar a mintuna 30.

No comments:

Post a Comment