Friday, 22 March 2019

Yadda zakayi idan babu wanda ya damu da kai

Wasu lokutan abu ne mai sauki kaji cewar kamar babu wanda ya damu da kai. Kai har ma mutane masu jama’a da yawa sukan yi tinanin anya kuwa da gaske mutanen da suke tare dasu sun damu dasu kuwa. Ka koyi yadda zaka rabu da wannan tinanin mai shakka, sannan ka darajta kanka.

 A takaice

Zamu tattauna akan wadannan abubuwan
- Ka koyi ganin darajar kanka.
- Ka kori yanayin jin cewa baka da daraja.
- Ka nemi tsofaffin abokanai da mutanen kirki.
- Ka gane yanayin rashin damuwa.
- Ka nemi sababbin abubuwan da zasu kayatar da kai da kuma abokanai.
- Ka nemi taimako a yanar gizo.
- ka cigaba da tattara yanayin da ka kasance cikin farin ciki.
- kaje wajen da ake wasanni da raha.
- Kashe lokaci da dabbobi.
- Ka fahimci yanayin bakin cikinka.
- Ka shiga cikin kungiyar masu bakin ciki mai tsanani.
- Ka dinga rubutawa.
- Ka dinga motsa jiki da cin abinci.
- Ka nemi magani.


 Kashi na daya: Neman majingina da kuma darajta kai

 1. Ka koyi ganin darajar kanka. Yin hakan zai taimaka maka wajen ganin abubuwa daban da ka saba gani. Sannan zai taimaka maka wajen ganin dabi’u masu kyau a wajen wasu. Zaka iya gwada wasu daga wadannan abubuwan.
- ka yiwa kanka abubuwa na kulawa kamar yadda zaka yiwa karamin yaro.
- ka dinga tinawa kanka cewa ba kai kadai bane
- ka dinga bawa kanka damar cewa mutum 9 yake bai cika 10 ba.

2. Ka kori yanayin jin cewa baka da daraja. Duk mutumin da yake ganin cewa bashi da daraja to yarda da cewa mutane sun damu dashi zai yi masa wahala sosai. Kar ka damu da abinda wani ya fada maka, kai dai kayi kokarin ganin darajar kanka.

3. Ka nemi tsofaffin abokanai da mutanen kirki. Idan ‘yan uwanka ko abokananka basa tsaya maka idan abu ya faru kayi tianin mutanen da ka sani masu kirki a baya. Zata iya yiwuwa malaminka ne, makwabci ko aboki.

4. Ka gane yanayin rashin damuwa. Idan kana cikin irin wannan yanayin, zaka dinga tinanin cewa mutane basu da kirki ko kuma suna wulakanta ka. Yawanci ba haka bane, mutane suna fuskantar rayuwarsu ne. Akwai lokacin da zaka kawowa mutum matsalarka sai yace maka “ai komai zai wuce” shi a wajensa yana tinanin taimako yake baka, kai kuma zaka iya tinanin wannan bai damu da kai bane.

5. Ka nemi sababbin abubuwan da zasu kayatar da kai da kuma abokanai. Idan kana tare da abokanain kadan ko kuma ‘yan uwa kdan, karamar matsala zata iya bata muku zaman tare da kuka saba yi. Saboda haka, ka nemi abubuwan da zaka dinga yi a lokatun da baka komai, kamar koyarwa, zuwa filin wasanni da sauransu.

6. Ka nemi taimako a yanar gizo. Akwai lokutan da kake bukatar kayiwa wanda baka sani ba magana domin samun saukin matsalarka.

7. ka cigaba da tattara yanayin da ka kasance cikin farin ciki. Idan kana cikin yanayi tasananin damuwa yawancin abubuwan da za’a yi maka na kulawa zaka manta sune bayan ‘yan awanni kadan. Saboda haka, abinda zai taimaka maka shine yanayin farin ciki da ka kasance a baya.

8. kaje wajen da ake wasanni da raha. Kar ka dinga kallon finafinan da zasu saka ka tausayi ko yin kuka. Ka nemi wasanni na abin dariya da sauransu.

9. Kashe lokaci da dabbobi. Akwai ni’ima idan ka zauna a cikin dabbobi kana kallon yadda suke rayuwa.Kashi na biyu: ka nemi maganin bakin ciki mai tsanani (depression)

 10. Ka fahimci yanayin bakin cikinka. Idan kaji cewa baka da amfani ko kuma baka da rayuwa mai kyau ko a nan gaba, to kana cikin bakin ciki mai tsanani. Wannan cuta ce da kake bukatar neman magani wajen masana. Gane wannan matsalar da wuri zaisa ka sami waraka da wuri. Da turanci ana nkiran wannan matsalar da depression.

11. Ka shiga cikin kungiyar masu bakin ciki mai tsanani. Su wadannan kungiyoyin suna taimakawa masu cutar bakin ciki mai tsanani.

12. Ka dinga rubutawa. Duk abinda ya faru da kai a cikin wannan lokacin yana da kayua ka sami littafi domin rubutawa. Amma ka dinga rufewa da abu na farin ciki. Misali, na hadu da wani a wajen shan shayi ya biya min kudin.

13. Ka dinga motsa jiki da cin abinci. Abimci mai kyau da kuma motsa jiki suna taimakawa wajen cire mutum daga cikin bakin ciki mai tsanani.

14. Ka nemi magani. Yana da kyau ka nemi likita domin ya baka magani ko ya hada ka da likita dake kula da tinani domin yi maka abinda ya dace.
No comments:

Post a Comment