Saturday, 9 February 2019

yadda zakayi idan aka yaudareka/ki ko cin amana


Yana da ciyo idan aka yaudari mutum. Yaudara tana iya zuwa daga dan ‘uwanka, babban abokinka, masoyi/ya ko wanda kuke aiki a waje daya. Akwai hanyoyi da zakabi domin ka samu nutsuwa bayan an yaudareka.


Mataki na daya: kula da kai


1. Kaji ciwon abun. Bayan an yaudareka zaka iya kasancewa cikin fushi, da kuma damuwa. Rike abun a ranka yana iya jawo maka abu mara kyau a lafiyarka da kuma ma’amalarku da mutumin. Ka fadawa kanka abunda ya faru ba tare da yanke hukunci ba. Zaka iya rubuta abinda ya faru ko kuma yadda kake ji a wannan lokacin. Zaka iya tura musu wasika akan abinda ya faru amma kuma kar ka tura wasikar sai kamar bayan satui daya. Wasu mutanen suna iya kamuwa da cutar matsalar bacci, ko ciwon zuciya ko jin zafi sosai idan sukayi kokarin danne abinda akayi musu, idan kna cikin wadannan mutanen to sai kayi hankali.

2. Ka daukarwa kanka lokaci. Yana da wuya idan wanda ya yaudareka kuna haduwa kullum ko kuma kuna tare ne ma. Idan hakane kuwa, sai ka nemi ya dan baka waje na wasu lokuta, idan kuma gida daya kiuke zaka iya komawa wani dakin ka dinga kwana.

Idan kuma wanda yayi yaudarar yana nesa ne, sai ka rage nemansu na dan lokaci. Zaka iya fada musu cewa zaka kirasu idan kana san yin magana, idan kaga hakan yayi maka aiki sai ka saka ranar da zaka kira.

Idan kuna haduwa a yanar gizo ne, sai ka rage shiga wajen da kasan zaka gansu ko kuma ka wani abinda zai dinga tina maka dasu.

3. Kar kayi saurin daukar matakin chanza rayuwa gaba daya. A gaskiya yaudara tana juya duniyar mutum ne bai-bai. Bayan ka rasa yardar da kayi wa mutumin wata zuciyar zata iya ce maka kawai ka yanke rayuwarka daga tasa. Ka dinga daukar lokaci kafin yanke irin wadannan manyan hukunce-hukuncen kamar sakin mata, chanza aiki, disga wani a cikin mutane da sauransu.

4. Ka guji daukar fansa. Akwai lokutan da zakaji cewa zaka iya yin komai wanda zai iya cutar da kanka ko kuma wanda ya yaudareka, idan hakan ya faru sai ka nemi taimakon masana. A hakikanin gaskiya babu yawancin daukar fansa ba abu ne mai kyau ba musamman wanda aka yishi a lokacin fushi. Lokacin da zaka bata kana tinanin daukar fansa shine lokacin da ka hana kanka walwala da jin dadi.

5. Ka nemi wanda zaka iya fadawa komai. Idan ka tattauna yaudarar da akayi maka da wanda ka yarda dashi yana taimakawa sosai. Abokin kirki, ko wani masani ko dan uwanka zai taimaka wajen wanke maka tinani akan matakan da zaka dauka. Ka tina cewa dan an yaudareka sau daya baya nuna cewa bazaka iya yarda da kowa ba kuma. Wasu lokutan ma ana iya kara yarda da mutumin daya yaudareka din.

6. Ka lura da kanka. Kula da kanka yana taimkawa wajen warkewa daga yaudara. Ka dinga cin abinci mai kyau kuma kana samun bacci mai dadi. Idan kana iya motsa jiki ma zaka iya dan tabawa domin samun chanjin yanayi da kuma samun bacci. Idan baka saba motsa jiki ba, zaka iya fita ka dan yi tafiya a kasa.


Matakai na biyu: ka dauki matakin yafiya

7. Kayi kokarin yafiya. Yin yafiya baya nuna cewa yaudara ba komai bace ko kuma bakaji zafin hakan ba. Hakan yana nuna cewa kana iya ci gaba da rayuwarka. Yin yafiya yana sawa wanda ya yaudareka yaji tausayinka da kuma cewa abinda yayi ba mai kyau bane. Kai kanka zakafi samun nutsuwar zuciya idan baka rike da kowa a ranka.

Masana sun gano cewa yin yafiya yana rage hawan jini, yana kara lafiyar zuciya, yana kuma rage kunci da damuwa.

8. Ka cire abu mara kyau daga zuciya. Abu ne mai kyau ka dinga tinanin kanka ba wai wanda ya yaudareka ba. Ka dinga fadawa kanka cewa wanda ya yaudareka ba shine yake juya maka rayuwa ba domin kuwa idan ka rike shi a rai, zai ta zageye ne a ran naka. Idan kayi tinanin mara kyau kar kayi kokarin danne shi, abu mafi kyau shine ka barshi ya shigo, ka gaishe da tinanin sannan ka fada masa ya kyale ka. Idan ya kara zuwa, ka barshi sannan ka kara fada masa ya tafi.

Idan kana samun wahalar yin hakan, zaka iya yin motsa jiki na (yoga) ko kuma (meditation).

9. Ka fadi yafiyar ko da kuwa ga kanka ne. Yin yafiya watakin kula da kai ne. Ba sai ka furta wa wani ba. Idan kaji kana san ka fada, zaka iya fadawa mutumin daya yaudareka cewa ka yafe kuma ka cigaba da rayuwarka. Idan kuma baka da ra’ayin ku cigaba da magana ko mu’amala ka fadawa kanka cewa ka yafe zai taimaka maka daga jin zafin yaudarar.

Idan bazaka iya fada musu da baki ba, sai ka rubuta musu wasika ko kuma ka tura musu sako na waya, amma idan kaga kana kara jin fushi a lokacin da kake rubuta wasikar, sai ka ajiye ka bari zuwa wani lokacin sai kaci gaba.

10. Ka yafe ba tre da kara ginawa ba. Zaka iya yafewa wanda ya yaudareka ba tare da kun kara dora rayuwarku ta da ba. Wani lokacin idan akaci amana hakan yana iya kawo karshen soyayyar ko mu’amalar. Kamar yadda na fada a baya, yin yafiya baya nuna cewa ba’a bata maka ba.

Idan wanda ya yaudareka yaki tuntubarka ko kuma ya mutu, sai ka yi yafiyar ba tare da taimako ko saninsu ba.

11. Kaci gaba da gwadawa. Idan kana samun matsalar ci gaba da rayuwa, ka tina cewa yafiya tana iya daukar lokaci. Idan ma yaudarar babba ce zata iya chanza maka rayuwa idan kayi wasa. Saboda, haka ka dinga tina abubuwan alkhairi daga mutumin yayin da zaka yafe masa.


Mataki na uku: kara gina yarda

12. Ka zayyana abbuwan da akayi na yaudarar. Da zarar ka zayyana abubuwan da akayi mak na cin amana ko yaudara, sai ka fadawa wanda yayi maka su din. Ka dinga amfani da lafazin da zai juna kanka ba wai shi wanda yayi yaudarar ba. Misali,

Maimakon kace “Kaci amana ta da ka fadi sirrin dana fada maka” zaka iya cewa “Ban ji dadi ba da kaci amana ta ta hanyar fadar sirrin dana baka amana”. idan baka iya fadar ra’ayinka, zaka iya rubutawa a takarda sannan ka bashi ya karanka kafin ku fara wata magana.

13. Kasa a nemi yafiyarka. Idan kana so kuci gaba da rayuwa da wanda ya yaudareka, ya kamata ka tabbatar cewa shima ya shirya kuci gaba. Idan wanda yayi yaudarar bai shirya daukar laifi ba ko kuma yana kokarin dora maka laifin hakan yana nuna cewa basu shirya aci gaba ba.

Anan wajen ma kayi amfani da lafazin da zai nuna kanka. Misali, ‘Bansan me nayi da za’a yaudareni haka ba, ina jira ka bani hakuri domin hakan zai taimaka sosai’.

14. Ku dauki darasi. Idan duk kun yarda zakuci gaba da rayuwa tare, sai ku tattauna abubuwan da suka faru cikin lumana da kwanciyar hankali. Kar ku tsawaita akan wajen da yafi jawo ciwo sosai amma dai ku tabbatar kun tattauna abinda ya faru, menene ya jawo faruwarsa da kuma dalilin dayasa yayi maka zafi a ranka.


A takaice

Idan an yaudareka ko anci maka amana sai ka dauki wadannan matakan.

- Kaji ciwon abun.
- Ka daukarwa kanka lokaci.
- Kar kayi saurin daukar matakin chanza rayuwa gaba daya.
- Ka guji daukar fansa.
- Ka nemi wanda zaka iya fadawa komai.
- Ka lura da kanka.
- Kayi kokarin yafiya.
- Ka cire abu mara kyau daga zuciya.
- Ka fadi yafiyar ko da kuwa ga kanka ne.
- Ka yafe ba tre da kara ginawa ba.
- Kaci gaba da gwadawa.
- Ka zayyana abbuwan da akayi na yaudarar.
- Kasa a nemi yafiyarka.
- Ku dauki darasi.

No comments:

Post a Comment