Saturday, 23 February 2019

yadda zaka boye gabanka idan ya tashi a cikin mutaneAbin kunya ne ace gaban mutum ya tashi a cikin mutane. Amma kuma mu sani cewa abu ne da aka hallice da namiji dashi, musamman a shekarun balaga. Akwai hanyoyin da zaka iya mutunta kanka kar mutane su lura da abinda yake faruwa da kai.A takaice

A wannan lokacin zamu tattauna:
- Ka saka boxers mai matse jiki. 
- Ka rufe gaban naka da wani abu mai fadi.
- Kayi amfani da doguwar riga.
- Ka daura rigar sanyi a kugunka.
- Danne ta aljihunka.
- Ka saka shi a hantsar wandonka.
- Ka harde kafafunka.
- Ka mikar da cinyarka.
- Yin amfani da abu mai sanyi.
- Yin fitsari.
- Motsa jiki.
- Ka kebence kanka.
- Ka dinga tinanin abunda bai danganci saduwa ba.
- Ka minstini kanka.Hanya ta daya: A saka kaya da suka dace.

1. Ka saka boxers mai matse jiki. Idan kana da gajeren wando ko boxers wanda zai matse maka jiki, shi ya kamata ka saka a ciki. Ka guji saka wanda yake da santsi ko kuma na leda, domin shima yana iya jawo abinda ba’a so.

2. Ka rufe gaban naka da wani abu mai fadi. Idan kana da jaka ko wani littafi ko laptop ko mayafi ko wani abu da zai iya zama akan cinyarka zaka iya amfani da su wajen rufe gaban naka. Hakan zaifi yi maka aiki idan kana zaune ne ko kana kwance.

3. Kayi amfani da doguwar riga. Idan kasan kana da matsalar saurin tashin gaba, sai ka dinga saka manyan kaya ko kuma riga ‘yar kanti mai tsayi wadda zata rufe gabanka.

4. Ka daura rigar sanyi a kugunka. Idan kana rigar sanyi kuma wannan matsalar ta faru da kai, sai ka daura ta akan kugun ka ta yadda zata rufe gaban naka. Hakan zai taimaka musamman idan akwai wanda yake kallon ka gaba-da-gaba.Hanya ta biyu: mayar dashi jikinka

5. Danne ta aljihunka. Zaka iya amfani da hannunka idan ka saka shi cikin aljihu wajen danne gaban naka domin mutane kar su lura. Ka ci gaba da danne shi har sai ya sauka ko kuma ya ragu ta yadda ba’a ganinsa.

6. Ka saka shi a hantsar wandonka. Ka saka hannunka a cikin aljihunka sannan ka dago gaban naka ka matse shi a hantsar wandonka. Hakan zai boye tashin gaban naka idan kana tafiya ko kuma kana tsaye. Amma kana bukatar wando mai belet (belt) ko kuma roba domin samun nasarar yin hakan.

7. Ka harde kafafunka. Idan kana zaune ne, zaka iya harde kafafunka domin ka danne gaban naka. Zaka iya jin babu dadi daga fari, amma kuma gaban naka zai sauka bayan wani dan lokaci.Hanya ta uku: a guji tashin gaban.


8. Ka mikar da cinyarka. Zaka iya mikar da kafarka (cinyarka) na sakanni kamar talatin, hakan zai janye jini daga gaban naka zuwa naman cinyar taka sai gaban naka ya sauka. Idan hakan baiyi aiki ba, ka cigaba dayi ko kuma ka hada da wata hanyar har gaban naka ya sauka.

9. Yin amfani da abu mai sanyi. Yin wanka da ruwan sanyi yana rage tashin gaban naka. Idan ba’a gida kake ba, zaka iya saka abu mai sanyi a gaban naka kamar ruwa mai sanyi ko lemon gwangwani mai sanyi. Idan ma aka kai mutum asibiti cewa gabansa yaki sauka sama da awanni hudu, suna amfani da sanyi ne wajen saukar da shi.

10. Yin fitsari. Wasu lokutan idan mafutsara ta cika zata iya jawowa ganban mutum ya tashi. Hakan yana faruwa musamman idan mutum ya tsahi daga bacci. Idan kana samun wahalar yin fitsarin, zaka iya watsa ruwa mai dumi domin ya taimaka maka.

11. Motsa jiki. Idan ka motsa jiki ba mai tsanani ba kamar dan fo-foti, tuka keke suna iya janye jini daga gaban naka wanda zai sa ya sauka. Idan kana jin kunyar fita waje sai ka dan motsa jikin a cikin dakin ka.

12. Ka kebence kanka. Idan aka dauki lokaci gaban naka zai sauka da kansa, saboda haka, zaka iya samun waje ka zauna kai kadai har hakan ya faru. Idan ma kana cikin mutane ne, zaka iya tafiya cikin bandaki har gaban naka ya sauka.

13. Ka dinga tinanin abunda bai danganci saduwa ba. Ka dinga kokarin dauke hankalinka zuwa wajen wani abu da zai rage maka tinanin saduwa kamar lissafi, ko wasanni. Ka mayar da tianinka wajen wannan abun har tianinka ya koma kansa gaba daya

14. Ka minstini kanka. Idan kaga tinani yayi maka yawa har gabanka ya fara tashi, zaka samu wani waje ne a jikinka kamar hannunka ko cinyarka ka minstini kanka sosai da mugunta. Zafin zai taimaka wajen dauke tinanin naka har gaban naka ya sauka.


No comments:

Post a Comment