Saturday, 16 February 2019

Yadda ake miyar dankali da kifi
Abubuwan da ake bukata

Dankalin turawa
Karasa
Kifin gwangwani ko sukunbiya
tumatir
attaruhu
albasa
gishiri
curry
maggi
gishiriYADDA AKE HADAWA

Da farko zaki  markada kayan miyarki tumatir, attaruhu da albasa,saiki dora mai a tukunya yayi zafi saiki zuba markadanki,ki fere dankaliki ki yanka gida biyu a tsaye,ki kankare karas dinki ki yanka a tsaye,idan kayan miyanki ya tafasa saiki zuba dankainki a ciki kisaka maggi gishiri curry. idan dankalin ya dahu saiki zuba kifinki a ciki da karas karas,saiki rage wuta.idan karas din yayi laushi saiki sauke.
Anaci da cous-cousNo comments:

Post a Comment