Friday, 1 February 2019

yadda ake gujewa fyade a gidaFyade abu ne mai ban tsoro kuma laifi ne babba a wajen shari’a. babu wata hanya ta tabbas da zaki dauka domin ki guje masa amma kuma akwai matakai da zaki kare kanki daga aukuwarsa. Zamu tattauna akan abubuwan da zakiyi domin kare kanki a gida.Mataki na daya


1. Mu gane cewa laifin mai fyaden ne. Da farko yana da kyau ki saka a ranki cewa duk wanda akayiwa fyade to ba laifin kowa bane sai na wanda yayi fyaden. Shari’a bata duba cewa baki saka hijabi bane ko kuma kinyi shigar banza domin kuwa hakan ba shine yake asalain dalilin fyaden ba. Amma kuma kinsan cewa shiga ta mutunci tana rage aukuwar hakan.

2. Mu gane cewa kariya daga fyade shine mu koyawa mutane su daina yi. Fyade zai ci gaba da auku a garuruwanmu har sai mun mutane sun daina yin fyaden. Saboda haka, mu wayar musu da kai akan illar yin fyaden domin su daina.

3. Mu gane cewa mata ma suna fyade. Ba wai kowanne lokaci ne maza suke yiwa mata fyade ba, mata ma ana samu suna yiwa maza fyade. Saboda haka kowa yana cikin hadari duk da cewa ba’a fiya samun mata sunyiwa namiji fyade ba a garuruwanmu.

4. Mu tina abu mara kyau yana iya faruwa ga mutanen kirki. Dan muna ganin cewa muna bin dokokin addini danan kasa baya nuna cewa baza’a jarrabe mu ba. Saboda haka, abu mafi kyau shine mu kare abubuwan da zasu jawo mana fyade duk da cewa babu wata sahihgiyar hanya kamar yadda na fada a baya.

5. Kar tsoron fyade ya hana mu rayuwa. Ya kamata mu kwantar da hankalin mu, mu huta, muyi wasa, mu ji dadin rayuwarmu ba tare da tinanin cewa za’a iya yi min fyade yau fa. Muyi shiga wadda ta dace, muyi abokanai maza da mata sannan ayi soyayya.Mataki na biyu: Gujewa fyade idan mun san mutumin


6. Mu fadawa wani babba. Idan munga alamun bamu yarda da wani a gidanmu ko danginmu ba, zamu iya fadawa wani babba da muka sani. Idan mukaga alamun cewa basa jin maganar mu sai mu sami wani mu fada masa kamar iayaye, malamai, iyayen kawaye da sauran mutanen da muka yarda dasu. Ya kamata ace muna cikin tsaro da aminci a cikin gidajen mu. To idan hakan bai faru ba menene amfanin kiransa gidanmu.

7. Mu guji zama daki daya da wanda bamu sani ba. Yawancin mutanen banza zaka gansu sun dau wanka sun fito waje tsaf-tsaf. Amma kuma idan kuka kebe ko kuma suna tare da wanda suke son lalatawa nan zasu nana kalar su ta gaske. Bai kamata mu dinga gayyatar mutanen da bamu sani sosai ba izuwa gidajen mu. Idan ma yawo zamuyi dasu, to muje wajen da yake da jama’a kamar wajen cin abinci, wajen shakatawa, wajen shan shayi da sauransu. Kar mu dinga amsa gayyatarsu zuwa wuraren da bamu yarda dasu ba.

8. Mu yarda da kanmu wasu lokutan. Akwai lokacin da jikinmu zai bamu cewa bamu yarda da wane ba, hakan yana iya zama gaskiya. Saboda haka, idan jikinmu ya bamu hakan zamu iya yarda da hakan domin kare kanmu. Mu guji mutane wadanda…
- Basa yarda ace musu A’A.
- sai sun jawo ra’ayinka kayi abinda kake ganin bai dace ba. (Misali, ‘kai banza ne kazo mu hau saman akwai dadi sosai’ da sauran maganganu.)
- Masu saurin fushi idan anyi abu ba dai-dai ba.
- suna yin maganganu wanda absu dace ba akan jikinki/ka ko wasu.
- Masu fara shegantaka idan sukaga mutane basa gani.

9. Muyi hargagin kiran dauki ko ‘yan sanda idan basu tafi ba. Idan yaki jin maganarki ai zaiji maganar ‘yan sanda saboda haka kiya hanzarin kiransu. Idan kuma babu halin hakan ki gudu waje kiyi masa ihun barawo domin shine ihun da mutane sukafi saurin ji.Mataki na uku: Ga wanda bamu sani ba

Yana da wuya ace mutumin da bamu sani ba ya shigi gidanmu yin fyade, duk da cewa ana samun hakan.

10. Mu dauki matakai. Mu tabbatar da cewa mun kiyaye gidajen mu daga masu yin gfyade. Misali…
- Mu dinga kulle kofofi da tagogi
- Idan wani yayi sallama mu tabbatar kafin mu bude masa kofa.
- Idan ki/kai kadai ne babu kowa kiyi kamar cewa akwai wani a gidan bayan ke/kai.
- Mu kunna fitulu idan dare yayi.

11. Muyi makwabta na kirki. Mu tabbatar muna zaman lafiya da makwabatan mu sannan su zame mana na gari domin idan abu ya same mu sune wadanda zasu fara kawo mana dauki. Zasu dinga kula da gidanmu idan bama nan. Ballantana ma yana da kyau ace muna da abokanai ko kawaye.

12. Mu nemi dauki idan mukaga alamun babu lafiya. Misali kin dawo gida daga sai kikaga alamun an shiga gidan ko wani da ya baki alamun haka, kar ki shiga gidan sai kii nemi tallafin wasu muatnen.

13. Mu bargidan idan ya zama dole. Idan mukaga wani yana binmu ko wani abu mai kama da hakan, sai mu fita daga gidan domin mu shiga cikin jama’a. idan mukaga hakan bai hana shi ba sai muyi masa ihu.A takaice

Idan muna gudun fyade a gidajenmu sai mu lura da wadannan abubuwan:
- Mu gane cewa laifin mai fyaden ne.
- Mu gane cewa kariya daga fyade shine mu koyawa mutane su daina yi.
- Mu gane cewa mata ma suna fyade.
- Mu tina abu mara kyau yana iya faruwa ga mutanen kirki.
- Kar tsoron fyade ya hana mu rayuwa.
- Mu fadawa wani babba.
- Mu guji zama daki daya da wanda bamu sani ba.
- Mu yarda da kanmu wasu lokutan.
- Muyi hargagin kiran dauki ko ‘yan sanda idan basu tafi ba.
- Mu dauki matakai
- Muyi makwabta na kirki.
- Mu nemi dauki idan mukaga alamun babu lafiya.
- Mu bargidan idan ya zama dole.

No comments:

Post a Comment