Friday, 1 February 2019

Yadda ake dambun kwai


Abubuwan da ake bukata:

- Kwai
- Nama
- Albasa
- Attaruhu
- Man Kuli
- Maggi
- Gishiri
- Curry
- Citta
- Tafarnuwa (Ga Mai bukata)Yadda ake hadawa:

Da farko ana bukatar a tafasa nama ta hanyar zuba masa Maggi, Gishiri, Curry, citta da albasa sannan a dora a saman wuta.
Idan ya dahu sai a kirba a turmi a jajjagi Attaruhu da Albasa a zuba akan dakakken Naman nan a kuma kawo dakakken Naman nan a zuba. Sai kuma a zuba maggi, curry, sannan a samu kwai mai dan yawa a fasa . sai a ajiye shi bayan an jujjuya shi. Daga nan kuma sai a dora kasko a saman wuta sannan a zuba man gyada a ciki a barshi har yayi zafi sannan a juye wannan hadin da akayi. Ayi ta juyawa har sai ya soyu kuma ya dagargaje. Shikenan sai a sauke.

No comments:

Post a Comment