Sunday, 17 February 2019

Yadda zaku zabi kayan da ya kamata ku saka a loqacin sanyiMun san cewa shi sanyi  yana da matsala sosai, musamman ma idan mutum ya tsufa. Saboda haka yana da kyau da sanyi mutum ya san irin kayan da zai saka saboda kare kansa daga jin sanyin. Idan muka ce kaya,  sun hada da; safar hannu data qafa, riga 'yar ciki, rigar sanyi, hular sanyi da sauransu. 1. Ya kamata  rigar da zaka saka a ciki ya zamanto cewa bata da nauyi kuma bata da kauri. Zata iya kasancewa wacce aka yi ta da auduga ko daga fata. 

2. Rigar da zaku saka a saman wannan ta zamanto cewa tafi ta cikin rashin nauyi amma kuma rigar sanyi ce, ta cikin ta akwai gashi gashi, kuma ya zama tana da mazugi (zip)  da zaku iya cireta loqacin da kuke so. 

3. Riga ta ukun da zaku saka ya zamanto wacce ruwa baya tsayawa a kanta ne, wacce ake kira da "nylon" a turance. 

4. Wandon da zaku saka ya zamanto mai dan kauri kadan kuma dogo sosai. 

5. Ya zamanto cewa kayan da zaku saka ana iya hangoku daga nesa, saboda ana samun dan duhu da sanyi, yana da kyau mutane su hangoka daga nesa musamman ababan hawa saboda tsaro.

6. Yana da kyau mutum ya samu abinda ake kira da headband domin kare sanyin da yake shiga ta kunne. 

7. Safa hannu biyu 2 ya kamata a saka, mai kauri da kuma mara kauri daga ciki. Ta yanda idan rana ta dan fito za'a iya cire mai kaurin dake sama a bar mara kaurin.

8. Game da hula kuwa yana da kyau a samu mai dan kauri wacce zata rufe har goshinka, ga masu ra'ayi zasu iya saka abinda ake kira da "face mask" domin rage sanyin kumatun su da hancin da kuma bakinsu. 

9. Yana da kyau safar qafa ta kasance mai kauri, irin wacce ake ninkawa biyu, ma'ana wacce take biyu a hade, saboda tafi bada dumi. 

10. Ga wadanda suke a yankin da akwai qanqara, yana da kyau su samu takalmi wanda yake ko ya shiga ruwa ba matsala, amma sunfi tsada sosai.

No comments:

Post a Comment