Saturday, 16 February 2019

Yadda zaku kula da motarkuMutane da yawa zasu so suji yanda zasu dinga kula da motocinsu domin daina basu wahala a yayin da suke amfani dasu.

Hanyoyin da zamu bi domin kula motocin mu sune:

1. Domin jin dadin motarku, ya zama dole ku dinga canza matatar fetir dinku (fuel pump)  duk yayin da kukayi tafiyar mil dubu arba'in.

2. Ku dinga canza birkin ku duk loqacin da kukai tafiyar mil dubu ashirin,  saboda rashin birki mai kyau kan zama hatsari ga lafiyarku da kuma lafiyar motar.

3. Ku canza baqin man ku duk loqacin da tafiyar ku, ta kai mil dubu uku saboda tabbatar da lafiyar motar.

4. Yana da kyau ku dinga goge mahadar batirin ku da motar a qalla sau 1 a shekara.

5. Idan kaga madaurin mutum na mota (belt). Ya tsufa, ko ya fara tsagewa, to ya kamata mai motar ya canza su baki daya.

6. Mutum ya dinga duba fitilolin sa koda kwai ya mutu. Ko daya ne ya canza shi

7. Ya dinga yawan duba  tayoyin sa koda akwai wacce ba iska sosai ko ta tsufa domin ya canza su.

No comments:

Post a Comment