Thursday, 7 February 2019

Yadda ake siyan data 1gb a N200 ko 4gb a N400 daga MTN


Bayani

Kamfanin MTN suna bawa kwastomomin su garabasar data domin su kara jawo zuwa kamfanin, amma kuma mutane da yawa basu san suwa ake bawa wannan garabasar ba kuma ya ake siyan wannan datar.

Yawancin masu amfani da waya a Najeriya a yau suna amfani da wayoyi manya kuma ta yaya za ku ji daɗin babbar wayar ba tare da samun damar yanar gizo ba.

'Yan watanni kadan, kamfanin Glo Nigeria sun kaddamar da Glo Yakata, shirin da ke bada masu amfani da Glo har zuwa 6GB na data kyauta duk wata idan suna saka kudi a layin.

Domin samun bayanin komai game da sabon MTN 4GB na N1000, 1GB don N200 da sauransu, na yi magana da mai kula da kwastomomi a MTN.

Don haka zan koya muku duk abin da kuke buƙar sani game da sabon MTN 4GB na N1000 da 1GB na N200 daga MTN.

Sabuwar Datar MTN

Sabon tsarin MTN din suna da tasaruka na kullum, mako-mako, da kuma wata-wata.

4GB a N1000
1GB a N200
250MB a N100Yadda ake siyan MTN 4GB a N1000, 1GB a N200, 250MB a N100

MTN 4GB a N1000 - Danna * 131 * 65 # kuma zaɓi 3 (yana expire bayan kwanaki 30)

MTN 1GB a N200 - Danna * 131 * 65 # kuma zaɓi 2 (yana expire bayan kwanaki 7)

MTN 250MB a N100 - Danna * 131 * 65 # kuma zaɓi 1 (yana expire a kwanaki 3)

Yadda ake gane cewa ka cancanta ka sayi MTN 4GB a N1000, 1GB a N200, 250MB a N100

Dukkan masu amfani da layukan zasu iya samun wannan garabasar amma kuma ba kowanne layi ne ya cancanta ya samu garabasar ba.

Kamar yadda mai kula da kwastomomin MTN ya zayyana min, layukan da ba’ayi mu’amalar kati a ciki ba na kwani 30 ko sama da haka sune kawai za’a iya bawa wannan garabasar.

Lambobin dana ambata a baya suna aiki ga kowanne layi amma ba sune ake duba cewa layi ya cancanta ko bai can canta ba.

Idan ka matsa lambobin dana ambata a baya, zasu bude maka shafin da zaka zabi irin datar da kake so ka siya, amma idan ka shiga sai su ce maka “Dear Customer, Enjoy data offers on MTN Deal zone, Dial *131*1#” wanda daga nan kuma sai su kawo maka shafin da zaka sayi datar da kowa zai iya siya kenan 1GB a N1000, 1.5GB a N1,200 da sauransu.

Yadda za a duba ko layi ya cancanta ya samu MTN 4GB a N1000

Don bincikawa idan MTN Sim dinka ya cancanta, kawai danna * 559 * 65 #

Sabda haka, idan kana da tsohon layin MTN, zaka iya kade masa ƙura kuma kayi amfani da wannan sabon tsarin.

 Idan ka gwada layinka baya yi, zaka iya siyan datar MTN 1gb a N500 Idan ka shiga nan

1 comment:

  1. Toh shi ne Kasan da Hakan kake sai da mani data da tsada

    ReplyDelete