Tuesday, 1 January 2019

Yadda Al-adun Aure Suke A Cikin Qabilu Daban Daban Na Nigeria

Nigeria qasa ce me tarin al’umma da yawa, wanda al’ummar ta sunkai sama da kimanin mutun miliyan 190, hakan ya saka aka samu qabilu daban daban a cikin qasar, wanda ko wannan su suna da al’adun su da yarikansu daban dana sauran. Zamu dauki yanda wadannan qabilu suke auratayya tsakaninsu da yadda al’adun auran wasu daga cikinsu yake.

QABILAR IGALA
Qabilar igala, qabila ce da mafi yawancinsu daga jihar kogi suke, amma aiki da auratayya ya saka sun bazu a cikin qasar Nigeria. Qabilar igala suna da al’ada ta in dai ba dole ba basu fiye bawa wani bare auran ‘ya’yansu ba. kamar yanda sauran qabilu suke da tsare-tsaren aure, suma qabilar igala suna da nasu.
Bude kunnuwanku kuji yanda suke neman auransu, koda kina/kana da sha’awar auran igala.

Idan saurayi yaga yarinya yana so, yakan je wurin iyayensa ya fada musu cewa yaga wacce yake so, su kuma iyayen zasuyi bincike akan dangin yarinyar domin su gano, ya dace ‘dan su ya hada zuriya da gidan ko bai kamata ba. Iyayen zasuje gidansu yarinyar idan sun yadda da tarbiyyar dangin ta, se suyi Magana da da iyayen yarinyar cewa ‘dansu yaga ‘yarsu yana so, idan sun yadda suna so a bashi izini ya fara ganin yarinyar. Suma iyayen yarinyar se sunyi bincike akan saurayin kafin su fara barinshi yaga yarinyar.TSARIN ZANCE A QABILAR IGALA
Suma suna zance kamar yadda yawancin al’dun qasar suke, amma tsarin zancen su yasha banban da dayawa daga cikin al’adun.  Idan sun baka yarinya ba zaka qara ganinta da wani sun zauna suna hira ba. Iyayen ta zasu tabbatar da hakan. Ga wanda baya son zance a wajen gida ko a kan hanyar da mutane ke wucewa, shi yafi cancanta daya nemi igala, domin igala basa barin ‘ya’yansu suyi zance a waje, se dai a cikin gida.

HIDIN-DIMUN AURE
Kamar yadda muka sani hidin-dimun auran qabilun Nigeria daban yake, ma’ana ko wacce qabila nata daban yake.
A qa’ida ta qabilar igala, mijin da zai auri yarinyar shi zai dau nauyin komi na gidan su yarinyar, tun daga abinda ya danganci abinda za’a ci a gidan su amaryar a loqacin bikin har ya zuwa duk abinda za’ayi na shaye shaye a gidan. Sannan maganar kayan daki ma kai zakayi, wannan dama ce ga wadanda suke so a kawo musu amarya kadai, ba tare da komi ba. Maganar lefe kuma ya danganta da qarfin mutun, idan kana da kudi zaka iya yin akwatu 50 babu damuwa amma in baka da kudi ko hudu ma ka kawo ya isa.

RANAR AURE (AL’ADA)
Mun san cewa cewa ko wacce qabila tana da al’adun ta da take gudanarwa kafin zuwan addinai.

Game da qabilar igala kuwa al’adarsu ita ce: ranar daurin auran, dangin amarya da ango zasu zo su zauna, za’a samo qatuwar tabarma a shimfida, a kan tabarma kuma se a samo qatuwar sabuwar atamfa a shimfida akai. Mun san cewa duk inda ake biki dole za’a samu kide-kide da bushe-bushe irin na murna da farin ciki, kai wani loqacin ma har da guda mata suke yi, domin nuna farin cikin su da jin dadin su. 

Amarya zata futo tare da qawayenta sun kewayeta, suna ta rawa, a haka zasu zo su gaida dangin angon, se su koma ciki, zata canza wasu kayan su qara dawowa su maimaita abinda suka yi a baya kamar yanda muka ambata, banbancin kawai wannan kayan da ta saka sun banbanta, zata qara komawa ta qara dawowa amma wannan karan da manya manyan qawayenta guda biyu (2), zasu zo su tsaya a gaban dangin bangarorin guda biyu. Za’a ce musu ku zauna mana ‘yan mata, se suce a’ah qugun tan eke mata ciwo, saboda da haka bazata iya zama ba, daga nan dangin angon zasu fara musu liqeen kudi, har sai sun ga damar zama sannan su zauna.
A daya bangaran kuma, wato bangaran angon, shima zai zo ta abokanshi guda biyu, in suka zo zasu tsaya a tsaye kamar yadda amarya tayi, wai suma sai an musu liqin kudin zasu zauna, qarshe dai ba abinda ake musu sai zuba musu idanu har su gaji su zauna. Suna borin kunya.

Daga nan ne kuma wakilin ango zai zo da sadaki da kayan shye-shaye da kuma goro, inda zai bawa dangin amaryar, sannan yace suna neman auran ‘yar su, iyayen amaryar zasu juya su tambayi amaryar, shin su karba ko karsu karba, zata ce musu, eh, su karba. Daga nan kuma biki ya qare, se a ci gaba da ciye ciye, da shaye-shaye da kuma kade-kade kai harda bushe-bushe har qarshen wannan rana.
Game da yanda suke aure a addinance kuwa,  ya danganta da irin addinin da suke bi.

No comments:

Post a Comment