Thursday, 31 January 2019

Yadda zaki sa mijinki ya dinga jin maganarki (bita zai-zai series)
Shin kina daya daga cikin matan da mazajensu basa jinsu idan sunyi musu magana? Ko kuma duk lokacin da kike so kuyi magana yana nuna miki bashi da lokaci? To yana da kyau ki san hanyoyin da zaki bi domin ya dinga jin maganarki. A wannan lokacin abinda zamu koya kenan.Mataki na daya


1. Ki zabi wajen da zakuyi magana wanda babu abinda zai dameku ko dauke hankali. Yawancin mata idan suna cikin damuwa suna saurin kiran mijinsu ne a waya, amma abinda basa ganewa shine, lokacin da suka kira shi basu san a cikin yanayin da yake ba. Zata iya yiwuwa an hada masa zafi sosai kinga kuwa yi masa magiya a wannan lokacin zai iya haifar da matsala.

Saboda haka, ki tabbatar da kin sami waje da babu wanda zai dameku, wajen da babu TV ko radio, idan da hali ma kar ki bari ya dauki wayarsa. Idan kuna da yara ki bari sai sunyi barci ko kuma sun fita wasa sannan kuyi maganar da zakuyi. Wannan yayiwa mata da yawa aiki.

2. Ki tambaye shi idan lokacin yayi masa. Akwa lokutan da baya san magana, yana jin bacci, yana cikin bacin rai, yana jin yunwa ko kuma wani abu makamancin haka. Idan maganar ba mai mahimmanci bace sosai sai ki tambayeshi lokacin da yaga yafi masa kuyi magana.

Ki zauna a gefensa ba a gabansa ko bayansa ba. Idan zakuyi maganar kar ki dinga zama a gabansa domin zaku dinga hada ido sosai wand azai iya jawowa kiji dan shakkar yi masa magana kadan. Wasu mazan kuma basa son a dinga hada ido dasu domin suna daukar hakan a matsayin raini ko yaya yake. Kuma kunsan yadda maza suke, san girma ne dasu (kamar gembo).

3. Ki nuna masa cewa maganar tana da muhimmanci sosai. Kina magana da mijinki ta wasa sosai, kuna dariya kuna tsokana. Saboda haka, idan lokacin magana mai muhimmanci tazo, ki nuna masa muhimmancin maganar ba wai wasa kikeyi ba. Akwai lokutan da zai nuna miki yana jinki amma kuma ba wai jinki yake ba, don haka ki tabbar ya gane muhimmancin maganar.

Nuna masa muhimmanci baya nufin cewa kiyi tsawa ko daga murya. A’a zakiyi amfani da murya ba irin wadda kikeyi idan kuna wasa ba.Mataki na biyu


4. Ki fadi maganarki kai tsaye, idan kun fara magana, kar ki dinga bugun daji kina kawo wasu dogwayen kissoshi da basu da amfani.

5. Ki guji yin mita ko kuma maimaita abu daya da yin mita. Misali idan abu kike so yayi, fada msa sau goma a dare daya ba zaiyi aiki ba, gajiya da jin maganar ma zaiyi kuma zai dauka ne kamar kin mayar dashi wani karamin yaro. Ana amfani da naci da mita ne wajen kama mutane, amma ba mijinki ba.

6. Ki tabbatar kema kina jinsa. Mijinki zai iya zama baya jin maganrki domin kuwa kema idan yana miki magana bakya saurarensa ballantana kiji abinda yake fada. Idan yayi miki magana ki dinga dan chanza kalaman kina maimaita masa su don ya tabbatar cewa kinji abinda ya fada miki kuma kin fahimta. Ki gane abinda yake fada miki baya nufin kin yarda da hakan. Misali:

Miji: “na gaji da yadda kike daga min muraya. Zakiga na dawo a gajiye amma kuma ki dinga daga min murya. Ni ba yaro bane. Wani lokacin ko zama bana yi kike farawa”.
Mata: “Naji kace baka son a dinga daga maka murya idan ka dawo gida daga wajen aiki musamman idan ka gaji, hakane?”

7. Ki tuntubi waliyan ki. Akwai lokutan da duk da kun gama magan da mijin naki matsala zata faru, ko kuma duk lokacin da kike magan baya daukar maganrki ko kuma baya duba yanayin da kike ciki ko zaki shiga. Saboda haka, sai ki nemi ganin waliyanki domin su baki shawara akan abinda ya kamata.Mataki na uku


8. Ki fahimci alamun soyayyarsa. Maza da mata akwai hanyoyin da suke magana kala-kala, amma hakan baya nufin daya yafi dayan. Mata sunfi saurin daukar chanji saboda haka suna saurin sabawa da yanayin da suka tsinci kansu a ciki. Su mata suna son a yaba musu, shi kuma namiji girmamawa yake so a soyayya. Su maza a al’adance sune shugabanni, su kuma mata sune masu nuna soyayya da kauna. Idan kika fahimci hakan zai taimakawa rayuwar aurenki sosai.

9. Ki lura da yanayin da yake son magana. Akwai mazan da basa son a zaunar dasu idan za’ayi magana, sunfi son ayi maganar idan ana tafiya ko idan kuna aikace-aikacen gida. Saboda haka, ki fahimci yanayinsa sai kiyi amfani da wannan damar.

10. Ki gano yadda yake so a girmama shi. A baya na fada maku cewa maza son girma ne dasu kamar gembo, su kuma mata suna so a dinga yaba musu. Idan kin kasance kina cikashi da girmamawa ta hanyar da yake so, to kin kashe macijin kuma kin sare kansa. Duk lokacin da kikayi masa magana zai dinga jinki.

A takaice

A lura da abuwan da muka tattauna a yau.
- Ki zabi wajen da zakuyi magana wanda babu abinda zai dameku ko dauke hankali.
- Ki tambaye idan lokacin yayi masa.
- Ki nuna masa cewa maganar tana da muhimmanci sosai.
- Ki fadi maganrki kai tsaye.
- Ki guji yin mita ko kuma maimaita abu daya da yin mita.
- Ki tabbatar kema kina jinsa.
- Ki tuntubi waliyan ki.
- Ki fahimci alamun soyayyarsa.
- Ki lura da yanayin da yake son magana.
- Ki gano yadda yake so a girmama shi.

No comments:

Post a Comment