Tuesday, 15 January 2019

Yadda zaka dinga yin doguwar hira da budurwarka a waya


Idan ka kasance mutumin da baka son magana sosai, ko kuma baka fiya yin surutu ba musamman a waya, kuma gashi kana da budurwar da ya kamata ka bata lokaci sosai kuna magana. To yana da kyau ka karanta wannan domin koyar yadda zaka yi doguwar hira a waya da budurwarka.

1. Ka dinga yi mata tambayoyi masu baukatar doguwar amsa. Su irin wadannan tambayoyin basa bukatar ‘E’ ko ‘AA’, suna bukatar doguwar amsa ne. Irin wannan hirar ce akeyi da kusan ko wanne irin mutum idan kana son kuyi doguwar hira.

Misalin irin wadannan tambayoyin shine ka tambayeta ‘Ya Yau?’ zata ce maka ‘Lafiya Kalau’. Amma idan ka ce mata ‘Bani labari akan wani sabon abu ko abu mai mahimmanci da kikayi yau’ anan ne zakaji ta fara baka labarai kala-kala.

Wani misalin shine kayi mata tambaya akan ra’ayinta akan fim din da dukanku kuke kalla. Misalai, zaka iya tambayarta ‘Me kike ganin zai faru da Lado a Episode 65 na fim din sabon salo?’

Bugu da kari shine, ka dinga neman shawara daga wajenta. Misali, idan wata matsala ta sameka sai ka nemi taimakonta da shawararta akan lamarin, shima hakan zai kara muku soyayya sannan kuma yasaka ku dinga hira mai tsawo a waya. Mata basu fiya son namijin da baya neman shawararsu ko taimakonsu idan matsala ta sameshi. Amma kuma ka sani cewa idan matsala bata sameka ba, kar ka kirkiro ta.

Misali na karshe shine, zaka iya tambayarta yadda take hango rayuwarta nan da shekaru kamar 30 haka. Ko kuma idan hakan baiyi aiki ba, zaka iya tambayarta akan rayuwarta lokacin tana shekara 8 da kuma abubuwan da take so lokacin.
2. Ka fada mata abubuwan da suka faru da kai a ranar. Idan wani abun farin ciki ya faru da kai ko kuma na bakin ciki, ko ma na bacin rai ne, yana da kyau ka dinga fada mata. Amma ka lura da cewa idan abun bacin rai zaka fada mata, kar ka dinga fada mata cikin bacin rai domin hakan zai zama kamar kana hucewa ne akanta.

3. Ku tsara abubuwa tare. Idan kuna ganin juna akan kari ko kuma kuna da damar fita shakatawa, zaku iya tattaunawa akan wuraren da zaku je da kuma abubuwan da zaku yi a wuraren.
4. Ka fada mata akan burinka na rayuwa. Idan kuna hira zaka iya fada mata akan burace-buracenka na rayuwa. Hakan zai taimaka wajen sawa hirar ta yi tsayi. Itama zaka iya tambayarta akan nata. Ko kuma ta baka labari akan burin da wasu suke dashi wanda hankali baya dauka (Misali a Fin din Ruwan dare).

5. Ka nemi karin bayani. Idan kaji tayi wata magana, yana da kyau ka nemi tayi maka karin bayani akan abinda ta fada. Hakan ba kawai zai sa hirar tayi tsayi bane, zai sa soayyya ta karu a tsakaninku domin zata ga cewa kana da ra’ayi akan abubuwan da taka fada maka.

6. Kayi nutsu domin ka ji maganganunta. Yana da kyau ka dinga jin maganganun da budurwarka take yi domin ka bata amsoshin da suka dace. Hakan zai sa taji cewa kana biye da ita.

7. Ka dinga cewa ta ci gaba da fada maka. Ka dinga yin amfani da kalamai kamar ‘Ci gaba da fada min’, ko kuma ‘Ya kika ji da hakan ya faru’, ko kuma ‘me kikayi bayan nan’. hakan zai bada kwarin gwiwar cewa taci gaba da baka labari
8. Ka dinga bada dama. Akwai wasu lokutan da kaine zaka dinga magan, akwai kuma wasu lokutan da ita zaka bawa dama tayi magana. Saboda haka, ka fahimci yadda kuke waya domin ka gane lokacin daya kamata kayi shiru domin tayi ta fada maka abinda zata fada maka.

9. Ka dinga bada amsa mai bukatar bayani sannan kuma mara hukunci. Misali anan shine idan tana baka labari akan yadda magenta bata da lafiya ko kuma ta mutu, zaka iya fada mata cewa ‘kasan cewa magen nan tana da muhimmanci a wajenta saboda haka kana jajanta mata’ hakan zai nuna mata cewa ka damu da labarin wanda zai jawo ta ci gaba da baka labarin.

10. Ka kwatanta cewa ka damu. Idan tana baka labari ka dinga kwatanta mata cewa labarin ya sosa maka zuciya. Zaka iya bata labarin yadda kaima irin wannan abun ya faru da kai, hakan zai taimaka mata. Amma kuma kar ka dinga zurfafa zance idan kana bata labarin yadda hakan ya faru da kai saboda hakan zai sa labarin ya zama naka bawai nata ba.

11. Ka san irin irin amsar da zaka bata. Akwai lokutan da idan ka bada amsa ko shawara, zata dawo kanka ne. Misali, idan tana baka labarin yadda tayi fada/rigima da kawayenta, kar ka kuskura ka ce mata ‘Gaskiya kawayenki basu da hankali’ saboda bazati ji dadi ba duk da cewa sunyi fada da ita. A maimakon ka fada mata haka, zaka iya cewa ‘Gaskiya kawayenki basu kyauta ba da sukayi fada da ke’. hakan zai sa taji cewa ka damu da ita amma baka zagi kawayenta ba.

12. Ka dinga tambayarta akan abinda ta taba fada maka a baya. Idan ka tina wani abu da ta taba fada maka, yana da kyau ka tambayeta akan wannan abun. Hakan zai nuna mata cewa ka damu da ita sannan kuma kana iya tina abubuwan da take fada maka. Misali, zaka iya ce mata ‘shin mama ta samu lafiya kuwa?’ ko kuma ‘shin kin samo sabon littafin nan kuwa?’

13. Kar ka dinga bada shwara sai an tambayeka. Yawancin maza idan sukayi magana suna bukatar shawara ne, amma mata idan sun baka labarin wata matsalar da take damunsu bawai suna bukatar shwara ne ba, sai dai yawanci suna son fitar da maganar dake ransu ne. Saboda haka, idan bata tambayeka shwara ba, kar ka dinga saurin bada shawarar. Amma akwai lokutan da zaka iya bada shawarar ko ba’a tambayeka ba.
A takaice:
- Ka dinga yi mata tambayoyi masu baukatar doguwar amsa.
- ka dinga neman shawara daga wajenta.
- Ka fada mata abubuwan da suka faru da kai a ranar.
- Ku tsara abubuwa tare.
- Ka fada mata akan burinka na rayuwa.
- Ka nemi karin bayani.
- Kayi nutsu domin ka ji maganganunta.
- Ka dinga cewa ta ci gaba da fada maka.
- Ka dinga bada dama.
- Ka dinga bada amsa mai bukatar bayani sannan kuma mara hukunci.
- Ka kwatanta cewa ka damu.
- Ka san irin irin amsar da zaka bata.
- Ka dinga tambayarta akan abinda ta taba fada maka a baya.
- Kar ka dinga bada shwara sai an tambayeka.

4 comments:

  1. Enter your comment...Eh gsky ne wannan yy kyau sosai da sosai

    ReplyDelete
  2. Gaskiya darasin nan ya koyamun abubuwa da yawa kuma ya koremun damuwata allah ya taimaka ya karabasira

    ReplyDelete
  3. Hakika wannan lacture tayi dadi haka kuma Na Kara samun ilimin yadda zan Dade ina farin ciki, saboda haka Allah ya saka da alheri ya kuma Kara mna budi ameen nagode da wannan darasi

    ReplyDelete