Sunday, 6 January 2019

Yadda Zaki Zama Yaya Ko Kwanwa ta Kirki Wajen Yan Uwanki
Ko kece babbar yaya, ko kuma 'yar tsakiya, ko ma 'yar auta ce, zamowa ta gari/kirka yana da matuƙar muhimmanci a rayuwa. Amma yin hakan yana buƙatar haƙuri, juriya, da kuma son juna. Sadarwa/tattaunawa tare da 'yan'uwanku zai haifar da alaƙa mai kyau tsakaninku a lokutan jin daɗi da kuma saɓaninsa.

1. Sadarwa/tattaunawa a lokuta masu yawa. Ko da kuna zaune a gida ɗaya ko ma a gari daban kuke, tattaunawa da juna abu ne mai amfani domin Ƙulla alaƙa mai ƙarfi. Wasu daga cikin hanyoyin sadarwa/tattaunawa sun haɗa da:

2. Ki guji tsokanar 'yan uwanki akan abinda basa so. Ki sani cewa tsokana abune da yake faruwa a tsakanin muatane, amma ki tabbatar idan kina tsokana kar ki dinga wuce gona da iri.

3. Rubutu saƙo ta waya ko kuma kira na bidiyo idan bakwa kusa da juna, ko da sau ɗaya ne a sati.
Ku ci abinci tare idan kuna zaune a kusa ko gida ɗaya.
Rubuta musu saƙo domin su san cewa kina tinaninsu ko suna ranki. Aika musu hotuna da zasu sa su nishaɗi ko dariya. Da dai sauran hanyoyi masu yawa.
4. Taimaka wa 'yan uwanki a lokutan da suke neman taimako. Idan kika ga misali sun kasa yin aikin da aka basu a makaranta, ko aikin gida, koma wani abu na kansu, a matsayinka na 'yar uwa sai ki taimaka musa. Kar ma ki dinga jira har sai sunce ki taimaka musu, zaki iya tambayarsu idan akwai abinda zaki taimaka musu dashi. 

Amma akwai lokutan da zaki ga basa so ki shigar musu, to a wannan lokaci sai ki mama kanki amma ki faɗa musu cewa idan suna neman taimako su kira ki.

5. Kuyi amfani da lokaci tare ku yi ayyukan jin daɗi da nishaɗi. Idan kun kasance tare ne, zaki iya shirya wani abu da zaku ke da su kawai domin jin daɗi. Zaku iya fita ko kuma kuyi a cikin guidanku. Amma sai kuyi abinda zakuji daɗinsa baki ɗaya. Misali, zaku iya:
- Kallon fim tare
- Wasanni na bidiyo ko na allo kamar drawut, ludo da sauransu
- Wasannin motsa jiki tare
- Yin rangadi tare bayan anci abinci
- Zuwa bakin ruwa/teku tare
- Girka abinci tare a gida 
- Yin zane da ƙirƙire-ƙirƙire
6. Gano abin da yake da muhimmanci a gare su. Zata iya yiwuwa ke da 'yan uwanki kuna da mabanbantan ra'ayi, na halayya, rayuwa da kuma bainda kowa yake so. Hakan baya nufin cewa bazaku iya jin daɗin rayuwarku tare ba. Ki nemo abinda sukafi so, ko kuma abinda sukafi bawa muhimmanci sosai. Sai ki taya su idan suna yi wata ranar. Misali:

Idan dan 'yan uwanki suna son kwallon ƙafa ne, sai ki tambayesu yaushe zasu kalla ko su buga domin ki taya su.
Idan kuma suna son wasnnin bidiyo ne, sai kice su koya miki wanda suka fi so domin kuyi tare.

7. Ki dinga tina ranar haihuwa da kuma lokuta na musamman. Wannan hanya ce mai sauƙi don nunawa 'yan uwanki cewa suna da mahimmanci a wajenki. Misali shine, tina ranar haiwuwa, aure, kammala karatu da sauransu. Zaki iya siyo musu katin gaisuwa domin ki basu. Ko kuma ki siyo musu kyautar abinda kika san suna so sosai. Yin kyauta ba sai da abu mai tsada ba.

8. Ki tsaya wa 'yan uwanki. Idan kinsan akai mutumin da yake/take basu matsala a ani abu, ki tambayesu ko zaki iya taimaka musu. Ko ki je kiyiwa mutumin magana, ko ki kai shi wajen hukuma. 
Amma idan a tsakaninsu ne suka jayaya. Kar ki kuskura ki ɗauki wani ɓangare daga cikinsu. Ki bawa wanda yake da gaskiya gaskiyarsa. Amma kuma kar ki bawa dayan haushi ta hanyar yin hakan.

9. Ƙarfafa gwiwa akan abu mai kyau. Idan kina 'yan uwanki sunyi abu mai kyau kar kiyi shiru kawai, zaifi kyau idan kika nuna musu cewa ki nlura da wannan halin nasu ko abinda sukayi mai kyau. Idan sun sami sakamako mai kyau sai ki taya su muran. 

10. Yin godiya idan sukayi miki abu. Idan 'yan uwanki sukayi miki alfarma ko sun ƙarfafe ki ki nuna godiyarki. Ki nuna musu cewa kin gani kuma kin yaba da abinda sukayi miki a rayuwa.
Alal misali, zaka iya ce, "Na gode da yawan saurarona da kikeyi lokacin da nake magana. Yana sa ni farin ciki da san cewa ina da 'yar uwa irinki

11. Sauraro idan dan 'yan uwanki suna buƙatar magana. A lokacin da wasu abubuwan suka faruwa a rayuwa, yiwa 'yan uwa magana zai iya taimakawa. Zaki iya sawa 'yan uwanki su faɗa miki abinda ke ransu idan kema kika faɗa musui wanda ke ranki.

Wani lokacin, mutum kawai yana buƙatar wani ya saurareshi ne, ba don ya bada shawara ba. Kafin ki bada shawara yana da kyau ki tambayesu idan suna son shawararki ne. Idan sun ce a'a, to kawai sai kiyi saurare.

Ki dinaga tabbatar musu cewa kina jin abinda suke faɗa. Misali idan suna magana sai ki dinga maimaita abinda suka faɗa lokaci bayan lokaci kamar ‘kenan sunƙi baki aikin da kika je nema’.

12. Koda yaushe ki dinga rufa musu asiri. Kar ki dinga faɗar sirrinsu indai kinsan babu wanda zai cutu da wannan abin.
13. Kafa iyakokinki kafin matsaloli su taso. Kar kiyi tsammanin 'yan uwanki su san iyakokinki ba tare da ki zayyana musu ba. Yana da kyau ki sanar dasu domin su guje shiga abinda ba kya so. Zaki iya nuna musu ta hanyar alama ko kuma ki fada musu da baki. Misali:
Zaki iya fada musu cewa duk idan kin dawo daga makaranta bakya son a dame ki sai kin huta na mintuna talatin

14. kiyi maganin rikice-rikice ta hanyar lumana. Idan faɗa ya auku tsakaninsu, to ki kwantar da hankalinki sannan ki haɗa tinaninki waje ɗaya kafin kiyi sulhu. Yi musu ihu baya raba faɗan yawancin lokuta. Kiyi musu magana cikin lumana da kamala, ki guji zagi ko zargin su.

kiyi magana da kwanciyar hankali amma idan kika ga kina ɗaukar zafi, zaki iya shiga ɗaki domin ki sauko.
Idan akan abinda baya buƙatar sulhu ne, zaki iya mayar musu dashi abun dariya ki wuce kawai.
Kar ki dinga tina faɗan da akayi a baya cikin sabuwar rigima.

No comments:

Post a Comment