Tuesday, 22 January 2019

Yadda Ake Yin Kwallon Taliya


Abubuwan da ake bukata:
- Taliyar Indomie
- Man Gyada
- Naman Sa
- Kwai
- Albasa
- Garin Busasshen Buredin
- Mai
- Gishiri
- Dakakken Barkon
- KoriYadda ake hadawa:
Za’a tafasa ruwa sai a zuba akan taliyar Indomie tayi kamar mintuna biyar ko hudu a ciki sai a tace ruwan a barta a cikin mataci, sai a dora mai a kan wuta a yanka masa albasa kamar guda daya, amma kar a bari ta soyu da yawa sai a nika danyen naman sa a iniji ko kuma a daka a turmi sai a zuba a cikin wancan dake kan wuta sannan a zuba Maggi, Gishiri, Curry da barkono da Filebon Indomie din a ciki a juya sosai, sai kuma a zuba hadin naman nan a cikin tatacciyar taliyar nan a juya a kawo garin busasshen Buredin a zuba sannan a juya sosai daga nan sai a duddunkula shi a dinga tsomawa a cikin ruwan kwai sa a barbadeshi da garin busasshen Buredin sai a soya a cikin mai. Idan ya chanza kala zuwa ja ko brown sai a sauke.
No comments:

Post a Comment