Tuesday, 22 January 2019

Yadda Ake Siyan Motar Da Akayi Amfani Da Ita


Siyan motar da akayi amfani da ita ba wani abu mai wahala kamar yadda mutane suke tinani amma fa sai kayi bincike sosai kar kaje ka siyi abinda zai baka wahala nan gaba.

1. Kayi tinanin aljihunka. Idan kayi niyyar siyan mota yana da kyau kasan nawa kake niyyar kashewa akan motar. Zata iya yiwuwa bashi zaka ci ko kuma kudinka ne, amma duk da haka kayi tinanin nawa kake da niyyar kashewa. Shawarar da zan baka idan zaka sayi mota akan zaka dinga biya da kadan-kadan shine kar ka doinga bayar da kudin da ya wuce kaso 20 na albashinka idan baka da wata hanyar samun kudin.

2. Ka tsara irin motar da zaka siya. Misali, idan ka kasance mutum ne mai doguwar tafiya a mota yana da kyau ka nemi motar da bata shan mai sosai kamar Toyota Corolla S. Idan kuma hawa duwatsu zaka dinga yi, yana da kayu ka nemi mota kamar SUV.
Saboda haka, kayi lisaafin abubuwan da kake so kamar mai cin fasinjoji da yawa, ko kuma ma hawa duwatsu ko kuma mara shan mai sosai.

3. Kayi lissafin kudin da zata ci idan za’a gyara ta. Mu gane cewa idan kan sayi mota mai tsada to lallai kayan gyaran ta suna da tsada. Saboda haka idan kasan baka samun kudi sosai, sai ka sayi motar da take da kayan gyaran ta suke da arha.

4. Ka duba kudin sauran motoci irinta. Idan kayi shawara akan irin motar da kake so ka siya, yana da kyau ka duba idan akwai wasu motocin masu irin abinda take dasu da kuma kudin. Akwai shafukan yanar gizo da zasu taimaka maka wajen duba kudaden motoci da kuma  sauran abubuwan da baza’a rasa ba. Kadan daga cikin wadannan shafukan sun hada da:

Zaka iya shiga www.jiji.ng ko kuma www.olx.com domin ka duba kudaden da sauran muatne suke siyar da irin wannan motar.

5. Ka nemi shigen motar. Misali idan kana son ka sayi kamar mota kirar sedan, kar wai ka duba Honda Accord kawai ko kuma Civic, yana da kayu ka duba sauran kamfanonim mota kamar Kia ko kuma Ford domin zaka iya samun kirar Sedan wadda take da saukin kudi.

6. Ka tuntubi dilan motocin da kayi amfani dasu. Akwai mutanen da su aikinsu ne kawai siyar da tsofaffin motoci. Yana da kyau ka nemi irin wadannan mutanen domin su baka shawara akan motar da kake son ka siya. Wani abin so a wajen manyan diloli shine zasu baka tabbas na cewa sun gyara komai dake damun motar kafin su siyar maka da ita. Amma fa irin wadannan motocin da suka gyara suna da tsada sama da sauran motocin da ba’a gyara ba.

7. Ka duba shafukan yanar gizo da ake siyar da tsofaffin motoci. Kamar yadda na ambata a baya shafuka kamar www.olx.com.ng, CarMax, AutoTrader da sauransu suna siyar da tsofaffin motoci. Bugi da kari, zaka iya amfani da shafin Facebook wajen ganin motocin da akayi amfani dasu. Bayan haka zaka iya tuntubar y’yan uwa da abokanan arziki idan sun san wanda yake da motar da zai siyar.

8. Ka gwada motar. Idan ka sami motar da kake so ka siya, yana da kyau idan da hali su baka motar tayi kamar kwana biyu zuwa uku a wajenka domin ka gwada ta. Ka hau manyan tituna da kananu domin ka tabbatar da lafiyar ingin motar.

9. Ka kira mai gyaran mota ya duba motar. Ko da ace dilan da zaka siya a wajen ya tabbatar maka da cewa ya gyara komai, yana da kyau ka kira makaniken da ka yarda dashi domin ya duba maka komai da ya kamata a motar ya tabbatar maka da cewa babu wata matasala. Idan baka da makanike da ka yarda dashi, zaka iya tambayar ‘yan uwa da abokanan arziki su hada ka da wanda suka yarda dashi.
Idan duk da haka ka kasa samun makanike da zai duba maka motar, akwa makanikai a shafin yanar gizo wanda zaka biya su domin su duba maka mota. Sannan kuma idan motar tana bukatar gyara yana da kyau su fada maka nawa motar zata ci domin ka sani.

10. Ka sa a ranka cewa ba iya kudin mota zaka niya ba. Ka sani cewa bayan ka sayi mota, sai ka biya mutane masu karbar la’ada, sai kayi mata rigista, sai kayi lasisin tuki, sai ka biya mata haraji da sauran abubuwa. Saboda haka, sai kayi tanadin wasu kudaden domin ka biya abubuwan dana ambata.

11. Kayi tayi akan motar. Idan ka sami motar da ranka yake so, ka taya domin kuyi ciniki sannan ka dinga neman ragi musamman idan kasan cewa an taba yin hatsari da motar ko kuma nayi mata fenti ne domin tajawo hankalinka. Ka saka a ranka cewa bawai dole ne sai ka siya daga wajen mutum daya ba, akwai sauran mutane da idan kaje zasu yi maka ragi. Idan baka da tabbas yadda kudin motar yake sai ka kirawo wanda ya san mota domin ya tayaka.

12. Kuyi yarjejeniyar dawo da motar idan kaga matsala. Bayan ciniki ya fada, yana da kyau kasan cewa garanti na kwana nawa zai baka akan motar sannan kuma yana da kyau ka rubuta domin ya saka hannu. Zama ka iya neman lauya domin ya tabbatar da gaske kake cinikin ka.

13. Ka tabbatar ka fahimci komai kafin ka saka hannu. Idan ka gama cinikin motar zakuyi yarjejeniya, yana da kyau ka fahimci duk wani da aka rubuta a jikin takardar, sannan kuma ka tabbatar da cewa ba’a bar wani waje daya kamata a cike ba kuma ba’a cike ba.

A takaice a lura da wadannan abubuwan:
- Kayi tinanin aljihunka.
- Ka tsara irin motar da zaka siya.
- Kayi lissafin kudin da zata ci idan za’a gyara ta.
- Ka duba kudin sauran motoci irinta.
- Ka nemi shigen motar.
- Ka tuntubi dilan motocin da kayi amfani dasu.
- Ka duba shafukan yanar gizo da ake siyar da tsofaffin motoci.
- Ka gwada motar.
- Ka kira mai gyaran mota ya duba motar.
- Ka sa a ranka cewa ba iya kudin mota zaka niya ba.
- Kayi tayi akan motar.
- Kuyi yarjejeniyar dawo da motar idan kaga matsala.
- Ka tabbatar ka fahimci komai kafin ka saka hannu. 

No comments:

Post a Comment