Friday, 25 January 2019

Yadda ake magance matsololin dake gidanku ko iyalanka
Yawancin mu mun girma ne a cikin ‘yan uwanmu. Kowa ya sani cewa matsaloli suna faruwa a cikin gidajen kowa da kowa. Bai kamata ace matsala tana faruwa a cikin gidanku sannan kuma baka dauki wani matakin ganin cewa kun magance wannan matsalar tsakanin ku. Yana da kyau mu tina cewa raywar nan duka nawa take da ba zamu zauna lafiya a cikinta ba, musammam ma tsakanin ‘yan uwanmu. Saboda haka, wasu daga cikin matakan da zaka dauka idan matsala ta auku a gidanka ko gidanku sun hada da abubuwan da zamu tattauna yau.
1. Kar kayi magana idan kana cikin fushi ko bacin rai. Ka sani cewa magan ko daukar mataki idan kana cikin bacin rai ko fushi yana jawo dana sani a yawancin lokuta. Saboda haka idan misali wasu ne suke jayayya ko fada a cikin gida, kar ka dauki mataki idan kana cikin fushi, ka bari har hankalin kowa ya dawo jikinsa sannan kayi abinda ya dace.

Idan zai dauke ka har kwana daya kafin ka sauko daga fushin da kake, yana da kyau ka dauki lokacinka wajen saukowa. Kar ka dinga gaggawar magana ko yanke hukunci idan kana cikin fushi domin idan aka sami matsala wannan jayayyar zata iya komawa gaba.

2. Ka tabbatar magana zakayi ba sako ba. Idan matsala ta faru a cikin gidanku, kar ka tura sakon E-mail ko SMS koma na WhatsApp. Daya daga cikin matsalar irin wadannan sakonni shine mutane basuji murayar ka ba, saboda haka zasu iya daukar cewa kana cikin fushi ne ko kuma kana magana ne a cikin bacin rai alhalin kuma ba haka bane. Bugu da kari shine mutane sukan fadi abubuwa a cikin sakon text wanda a gaske bazasu iya fada ba.

Saboda haka, shawara ta anan shine ka samu lokaci domin kaje ku tattauna matsalar da ta faru. Idan kuma baka kasar ne ko kuma garin, zaka iya amfani da kira na bidiyo domin su dinga ganin fuskar ka. Idan hakan bazata yiwu ba, to sai kayi amafni da kira na murya kawai. Amma kamar yadda na fada, kar kayi amfani da sakon text, wasika, e-mail, whatsapp da sauransu wajen magance matsalar da ke damun iyalanka ko gidanku.

3. Ka amshi laifinka da kuma na sauran mutanen. Idan kasan cewa kana da laifi, yana da kyau ka yarda da cewa kayi laifi domin a magance matsalar. Ka gane cewa, kowa yana iya jawo matsala a cikin gidansu, amma yarda da cewa ya jawo matsalar yana taka muhimmiyar rawa wajen magance ta. Domin kuwa, idan ma bai yarda yayi laifi ba to jayayya za’ayi tayi.

Shawara anan shine, idan ka sami matsala da wani a gidanku, koda shine da laifi zaka iya cewa “Naga kayi fushi, duk da dai cewa nima raina ya baci, amma kayi hakuri domin inaso mu magance matsalar, saboda haka, me kake bukatar nayi yanzu?”. Idan ka fada masa haka zakayi mamakin yadda zai sakko daga fushin da yakeyi.

4. Kayi yafiya idan an bata maka. Ka sani cewa yin yafiya musamman ga wanda ya bata maka a cikin gidanku ko iyalinka. Saboda haka, idan wani yayi maka laifi kayi hakuri, ka tina cewa ana iya chanza abokanai amma ba’a iya chanza ‘yan uwa. Idan da hali ma, ka sameshi domin ka jaddada masa cewa ka yafe masa amma kuma kar ya kara yi maka ( amma fa kar ka fada cikin bacin rai), hakan zaiyi abinda baka tinani. Idan kaine kuma kayi laifi ka nemi yafiya.

5. Ka gano tushen matsalar. Kayi kokarin gano menene ya jawo matsalar ko kuma menene yake jawota. Zata iya yiwu kana fama da matsalar rashin kudi ne, ko kuma kana fama da wata rashin lafiya da basu sani ba, ko kuma kuna cikin bakin cikin mutuwar wani dan gidanku ne. Saboda haka, kayi kokarin gano abinda yake jawo matsalar domin haka zai baka damar magance ta a saukake.

Yana da kyau kayi nazari akanka, ka gane cewa me yasa kake boye wata matsalar ka daga ‘yan uwanka, ko kuma me yasa mahaifiyarka tashe kashe kdui da yawa wanda yake damunka domin baka da sana’ar da zaka dinga bata wasu ba.

Kar ka dinga kintacen abinda wasu suke tinani, ka dinga tabbatarwa daga wajensu. Kaguji yin gulma da munafunce-munafuncen ‘yan uwanka domin idan maganr ta koma kunnensu bazasu ji dadi ba. Idan akwai wani da kafi yarda dashi a gidan naku kamar mahaifinka, yana da kyau ka fada masa matsalar domin ku magance ta.
6. Ka dinga tambayoyi domin kaji ra’ayinsu. Idan kana bukatar magance matsala yana da amafani da kasan ra’ayin sauran mutanen. Ka dinga yi musu tambayoyi wadanda zasu bukaci bayani sasai, amma kayi hankali kar ka dinga dora laifi idan kana yin tambayar. Misali idan kaga cewa ‘yar uwarka ta daina kiranka zuwa gidanta kamar yadda takeyi a baya, zaka iya cewa “naga kwana biyu haduwa tayi mana wahala, me kike tinanin ya jawo hakan?”. wani misalin shine idan kana bukatar bayani akan yadda mahaifiyarka take kashe kudi sosai, zaka iya cewa “Naga kwana biyu kina kashe kudi sosai akan kayn sawa, anya kuwa basuyi yawa ba?”.

7. Ka bude tattaunawa. Tattaunawa tana da muhimmanci idan ana son magance matsala. Idan ba’a zauna an tattauna matsalar da ke aukuwa ba, zata cigaba da faruwa ne. Saboda haka, ka zama jarumin da zaka bude kofar tattaunawa, idan kuma kaine karami zaka iya samun babba a gidan domin ya saka lokacin da zaku zauna ayi magana kaga kenan kaine ka fara daukar mataki.

Ka guji yin shaye-shaye kafin kazo tattaunawa domin hakan zai jawo matsala. Bugu da kari shine ka san lokacin daya kamata ku tattauna. Kar ka kawo korafinka a wajen da bai kamata ba.

8. Ka gane idan matsala ta kai ayi mata zama. Akwai alamomi da suke nuna cewa matsala ta kai a zauna a tattauna yadda za’a magance ta. Misali anan shien idan jayayya tayi yawa a tsakani, ko kuma idan an daina neman juna, ko kuma idan ana fushi da juna, a wasu lokutan ma idan anyi dambe. Yawancin jayayya tana faruwa ne saboda bam-bancin ra’ayi tsakanin mutane, misali banbancin akida, banbancin ra’ayin al’ada da sauransu.

9. Kayi kokarin kawo masalaha wadda ta dace. Idan matsala ta faru, yana da kyau ka kawo masalahar ta zatayi dai-dai. Abinda nake nufi shine ka kawo masalahar da kowai zaiji dadinta tsakanin mai laifi da kuma wanda aka bashi da laifin. Abu na farko da zaka farko ganowa shine, shin matsalar tana da masalaha wanda ya danganta ne da matsalar da kuma hanyar da akabi domin a magance ta a baya.

10. Kayi magana da mutanen daya bayan daya. Akwai lokutan da ba’a zaunawa gaba daya domin a tattauna matsalar da ta faru. A irin wannan lokacin, zaka kira mutanen gidan ne daya bayan daya domin ku tattauna matsalar. Dalili anan shine wani lokacin idan kuka zauna gaba dayanku domin ku magance wata matsalar wasu mutanen bazasu fadi ra’ayinsu ba domin kar wanda basu goyi bayansa ba yaji babu dadi, saboda haka sai kaji sunyi shiru. Amma idan ka samesu daya bayan daya anan ne zakaji ra’ayinsu na ainihi.

11. Ka kira duk mautanen gidan naku. Akwai lokutan da magana da mutanen gidanku daya bayan daya bata aiki, musamman idan matsalar ta shafi kowa ne a gidan naku. Misali idan matsalar kudi ce, ko matsalar rashin lafiyar wani ne, da sauransu. Kar a bari mutum daya ya dinga magana shi kadai idan ana tattaunawar.
12. Idan yaro ne shima kasan matakin da zaka dauka. Akwai matsalolin da suka shafi yara a gida. Misali basa tashi daga bacci da wuri, basa yin ayyukan gida da aka saka su, sun guduwa daga makaranta ko yana rashin kunya da sauransu. A wannan lokacin kiran yaron zakayi sannan kayi masa bayanin matsalar dalla dalla. Amma idan kana bayanin kar ka dinga nuna fushinka, misali idan zakayi masa magana akan rashin tashi da wuri zaka iya cewa “Munga alamar kwana biyu tashi daga bacci yana yi maka wahala wanda yake jawowa kake makara a makaranta, wannan ce matsalar da take bukatar gyara”. idan kana maganar kar ka nuna fushi ko kadan sannan kuma ka nemi shawararsa akan yadda yake tinanin za’a magance matsalar. Ka tabbatar ka gano tushen matsalar, misali shin chatting din dare ne yake hana shi tashi da wuri ko kuma menene.

13. Ka saka iyaka. Akwai wasu mutanen gidanku da suke jawo maka matsala a rayuwarka koda yaushe. Irin wannan lokacin zaka iya saka ka’idoji da iyaka a kansu. Misali idan ka gansu a cikin mutane zaka girmamasu amma idan kuna tare zaka nuna musu iyakar da ka saka musu misali cewa ka daina basu aran kudi ko kayanka domin suna lalata maka. Wannan yana cikin kyautatawarka ne wanda zaka iya dainawa a matsayin iyarkar da ka saka musu. Ka tabbatar da cewa ka fada musu dalilin dayasa ka saka musu iyakar amma a cikin lafazi mai dadi.

14. Kasan lokacin da zaka ja da baya. Akwai matsalolin da basu da masalaha, ko kuma an gwada masalahohi da yawa duk basuyi aiki ba. To a wannan lokacin sai ka hakura ka ja da baya. Misali idan kai gurgu ne kuma kayi kokarin zamatakewar ‘yan uwantaka da mutanen gidanku amma abin yaci tura, to a wannan lokacin zaka iya ja da baya domin kuwa kayi iya bakin kokarinka sune suka ki ka.

Saboda haka a lura da abubuwan da muka tattauna akansu
- Kar kayi magana idan kana cikin fushi ko bacin rai.
- Ka tabbatar magana zakayi ba sako ba.
- Ka amshi laifinka da kuma na sauran mutanen.
- Ka gano tushen matsalar.
- Ka dinga tambayoyi domin kaji ra’ayinsu.
- Ka bude tattaunawa.
- Ka gane idan matsala ta kai ayi mata zama.
- Kayi kokarin kawo masalaha wadda ta dace.
- Kayi magana da mutanen daya bayan daya.
- Ka kira duk mautanen gidan naku.
- Idan yaro ne shima kasan matakin da zaka dauka.
- Ka saka iyaka.
- Kasan lokacin da zaka ja da baya.No comments:

Post a Comment