Saturday, 26 January 2019

Yadda ake gina yarda da aminantaka (trust)
A hakikanin gaskiya gina yarda ba abu bane da zamuyi wasa dashi a rayuwarmu. Yarda da kuma amincewa da mutum yana iya kaiwa ka fada masa duk wani abu da yake damunka wanda idan wannan wanda ka yarda dashi ba mutumin kirki bane to zai iya kai ka ga hallaka.
1. Kasa a yarda da kai a farko. 


Idan kana so wani ya yarda da kai, to ai yana da kyau ka nuna masa cewa kaima kana da amana zai iya yarda da kai din. Zaka iya yin hakan ne ta hanyar misali nuna masa cewa ka yarda dashi ta hanyar fada masa ‘yan labarurrukan da suka shafeka kamar ‘yan matsalolin ka da kuma wasu ‘yan abubuwan da baza’a rasa ba. Idan ka gwada wannan akan wani sai kaga baya nuna sakamako mai kai ko kuma gaba daya ma baya san irin wannan alakar sai ka rabu dashi ka nemi wanda zaku yarda da juna tare.

Kar ka dinga yin karya idan kana kokarin gina yarda tsakaninku domin kuwa koda kananun karya suna iya jawo matsala nan gaba a cikin mu’amalarku.

Abu mai muhimmanci a wannan gabar shine ka bada labarin naka amma kar ka wuce gona da iri. Kasan lokacin daya kamata ka tsaya a labarin naka domin kuwa kana kokarin gina yarda ne ba wai kun yarda da juna gaba daya bane.

2. Gina yarda a lokaci mai tsayi. 

Ka sani cewa ita yarda ba kamar makunni bane da zaka kunna ko ka kashe idan kaga dama. Ana gina ta ne a lokaci mai tsayi. Domin gina yarda zaka iya farawa da taimaka masa da ‘yan abubuwan da baza’a rasa ba kamar rakashi wurare da kuma cika al-kawari musamman idan kun tsara zaku hadu to ka dinga zuwa a kan lokaci. Kar ka dinga yanke hukunci da zarar ka hadu da mutum.

3. Ka gina yarda matakai kala-kala a wajen mutane. 

Akwai mutanen da zaka yarda dasu ne kadan misali wanda kuke aiki a waje daya da kuma wadanda kuka hadu da su ba jimawa. Akwai kuma mutanen da zaka iya yarda dasu akan rayuwarka ma. Saboda haka, ka gane kalar mutane da kuma irin yardar da zaka basu.

4. Ka lura da abinda mutane suke aikatawa ba wai abinda suke fada ba. 

Kowa zai iya yin alkawari, amma kuma ba kowa ne zai iya cika wannan alkawarin ba. Saboda haka, ka dinga lura da halayya da dabi’un mutum ba wai kai abinda yake fada a baki ba. Zaka iya neman alfarma a wajensu ka lura zasu yi maka kamar yadda sukayi alkawari ko kuma bazasuyi ba.

5. Kaima kazama mai amana.

Idan kana son ku gina yarda ai kai dole ne sai kazama abin yarda. Misali idan kaima kayi alkawari baka cikawa ko kuma idan ya fada maka sirrinsa baka rike masa.
Idan an tambayeka wata alfarma wadda kasan za’a iya samun matsala to yana da kyau ka fada musu gaskiya, kar ka dinga yin alkawarin da kasan cewa babu tabbas. Amma ka nuna musu cewa zakayi iya bakin kokarinka.

6. Ka tina cewa dan Adam tara yake bai cika goma ba. Kowa yana yin abinda bai dace ba a wasu lokutan, wani lokacin suna faruwane ba da san ran mutumin ba. Misali, kin halartar zama da kuka shirya, ko kuma fadawa wani siirinka saboda jin dadin zance ko kumasu dinga san kansu a wasu lokutan. Idan kana san gina yarda ka duba yawancin abinda mutum yakeyi ba wai kuskurensa guda daya ba.

Idan kaga mutum kullum yana karya alkawari ko kuma idan yayi wani abu baya neman a yafe masa ko ya bada hakuri, to irin wannan mutumin yarda dashi zaiyi wahala sosai.

7. Ka yarda da kanka. Idan jikinka ko a ranka kaji cewa baka san yarda da wani, to ka yarda da hakan idan kuma kaji wani abin yarda ne to shima ka yarda da hakan har sai ka sami hujja da take nuna akasin yin hakan. Idan kayi hakan zai taimaka maka sosai.

8. Ka gane cewa mutanen da zaka yarda dasu suna cika alkawari. Akwai wasu mutane masu da’awar cewa ‘kaji abinda na fada maka ba wai abinda kaga ina aikatawa ba’ wannan ba gaskiya bane idan akazo fannin gina yarda. Ka lura da abubuwa uku a wajen mutane
- shin suna cika alkawarin da suka dauka?
- shin suna karsa ayyukan da suka saka kansu?
- shin suna tabbatar da cewa kuna gama tsare-tsaren da kuka ce zakuyi?

9. Ka gane cewa mutanen da zaka yarda dasu basa yin karya. Mutane makaryata suna da wuyar sha’ani. Dalili kuwa ba zaka taba gane abinda suke tinani ba. Yawancin makaryata zaka ga basa san kallon mutum a idonsa ko kuma zakaji suna yawan chanza yadda suka baka labari a baya. Masu fasaha sunce ita gaskiya bata bukatar ka haddace ta, amma kuma karya dole ne ka hardace ta saboda zaka iya manta abinda ka fada a baya. Saboda haka idan kaga mutum yana yin karya koda kuwa kananan karya ne to wannan mutumin bai kamata a yarda dashi ba.

10. Ka lura da yadda yake magana akan wasu. Idan kaji mutum yana yin magana kamar, ‘Kausar tace kar na fada….. amma kuma…..’ to irin wannan mutumin ko kusa ko alama ba abin yarda bane. Domin kuwa tinda ya fada maka sirrin wasu to kaima zai dauki sirrinka kuwa ya fadawa wasu. Idan kana ginin cewa kar wasu su yarda da wannan mutumin to ai kaima kar ka yarda dashi.

11. Ka gne cewa halin mutum daya bay nuna cewa kowa haka yake. Hausawa sunce wake daya shine yake bata gari, idan wanda ka yarda dashi yaci maka amana baya nuna cewa kowa haka yake a duniya. Akwai mutanen kirki a duniyar, saboda haka, kar ka bari mutum daya ya shafawa kowa bakin fenti.
12. Ka yanke hukunce a hankali. Idan wanda ka yarda dashi yaci maka amana kar ka dinga hanzari wajen yanke masa hukunci ba batanci a kansa. A’a ka dauki lokacinka wajen tabbatar da hujjojinka. Misali, zaka iya yiwa kanka wadannan tambayoyin:
- Shin wadanne hujjoji nake dasu a kansa?
- Shin hakan halinsa ne ko kuma me ya faru?

13. Mutane suna saurin manta alheri. Yana daga cikin dabi’un mutane su dinga saurin manta alheri idan anyi musu sharri koda kadan ne. Zaka iya rayuwa da mutum shekaru ashirin kuna kyautatawa juna amma daga rana daya idan yaci maka amana ko kuma yayi maka wani abu sai ka manta da wannan alherin da yayi maka na shekarun baya, kawi sharrin nan nasa zaka dinga tinawa. Shin kayi masa adalci?

A takaice mun tattauna akan wadannan abubuwan:
- Kasa a yarda da kai a farko.
- Gina yarda a lokaci mai tsayi.
- Ka gina yarda matakai kala-kala a wajen mutane.
- Ka lura da abinda mutane suke aikatawa ba wai abinda suke fada ba.
- Kaima kazama mai amana.
- Ka tina cewa dan Adam tara yake bai cika goma ba.
- Ka yarda da kanka.- Ka gane cewa mutanen da zaka yarda dasu suna cika alkawari.
- Ka gane cewa mutanen da zaka yarda dasu basa yin karya.
- Ka lura da yadda yake magana akan wasu.
- Ka gne cewa halin mutum daya bay nuna cewa kowa haka yake.
- Ka yanke hukunce a hankali.
- Mutane suna saurin manta alheri.

Kar a manta ayi COMMENT a kasa. 


No comments:

Post a Comment