Saturday, 5 January 2019

Yadda Ake Amfani da Shayi Wajen Mayar Da Sabuwar Tatakarda Zuwa Tsohuwa


A mayar da sabuwar takarda tsohuwa abu ne na bandariya da raha wani lokacin. Zaka iya mayar da takarda daya ko littafi gaba daya ya koma tshoho tawannan hanyar.

1. Ka saka ganyen shayi guda daya ko biyu a cikin kopin shayi. Amma ya danganta da yawan takardun da kake son ka rina zuwa tsofaffi. Saboda haka sai ka kwatanta, da takarda daya ganyen shayi guda daya. Amma idan kana son takardar tayi tsufa sosai to kana bukatar kamar ganyen shayi guda biyu a duk takarda guda daya.
- ka lura da kofin da zakayi amfani dashi. Ka tabbatar kayi amfani da kofin shayi na tangaran domin ka mayar da takardar tsohuwa. Ka guji amfani da kofin roba kona karfe saboda zai iya jawowa ka kone.

2. Mataki na biyu shine ka zuba ruwa a cikin tukunya. Ka lura kar ka zuba ruwa kadan saboda ruwa idan ya tafasa yana rage yawa. Saboda haka sai ka zuba ruwa kamar cikin kopi daya idan ganyen shayi daya zaka tafasa.

3. Mataki na uku sai ka kunna wuta ka tafasa ruwan. Idan kana so ka tabbatar da cewa ruwan ya tafasa, zakaga wasu kwaikwaye a saman ruwan. Amma idan kana amfani da butar dafa ruwane, to zakaji wata kara tana fitowa daga cikin butar. Kayi hankali sosai idan butar/tukunyar tana da marikin karfe domin zai iya kona hannu. Idan kuma yaro ne yake son tafasa ruwan, sai ya nemi taimakon na gaba dashi a shekaru.4. Ka saka ganyen shayin a cikin kopin. Bayan nan sai ka zuba tafshasshen ruwan a cikin kopin. Kar ka cika kopin har zuwa bakin, domin zai iya fallatsar maka. Sai ka jira kamar mintuna biyar domin ganyen shayin ya jiku sosai har ya koma kalar da kake bukata. Idan kana son yayi baki sosai, sai kayi amfani da ganyen shayi guda biyu, maimakon guda daya.

5. Kayi rubutu a jikin takardar. Sai ka dauko takardar da kake so ka tsufar kayi rubutun da kake so a jiki. Ka lura da cewa da zarar ka mayar da ita tsohuwa to bazata kara karbar wani rubutu sosai ba.

Ka tabbatar cewa inkin jikin takardar ya bushe kafin ka rina takardar. Domin ka saka takardar tayi kama da tsohuwa sosai, zaka iya dukunkune ta kadan sannan ka mikar da ita, zakuma ka iya yage gefen takardar. Hakan zai bawa mutane alamar cewa gaskiya tayi shekaru da yawa. Ko wacce irin takarda tana iya yi amma kuma takarda mai kauri bata bushewa da wuri kuma tana bukatar ganyen shayi sama da takarda mara kauri.

6. Ka saka tardar akan faranti. Amma ka samu faranti da yake da zurfi domin kar idan kana zuba shayin ya dinga zubowa. Sannan kuma ya kasance yana da tsayi da zai iya daukar takardar.

7. Saka ganyn shayin akan takardar. Zaka dauko daya daga cikin ganyen shayin ne ka dinga danna shi akan takardar har sai kaga babu shayi a jikinsa. Daga nan sai ka kara tsoma shi a cikin kopin shayin ka kara danna shi akan takardar. Zaka cigaba da yin hakan har sai ka danna a kan takardar gaba daya ko kuma ka saka a inda kake son ya tsufa. Amma idan kana so mutane sufi yarda, zaka iya kyale wasu wuraren sannan kuma kayi amfani da yan yatsunka wajen bada launuka kala-kala.

8. Ka juya takardar sannan ka rina bayanta. Rina bayan takardar zaifi bawa mutune alamar cewa takardar ta tsufane da gaske, ko da kuwa iya gaban kake son nunawa mutane.
9. Daga nan sai ka barbada garin TUMERIC idan kana so takardar tayi yalow. Amma fa kasani cewa barbada garin ba dole bane amma idan ka saka zai taimaka wajen fito da kaslar tsohuwar takarda.

10. Daga nan sai a barbada garin kofee ‘coffee’. idan bukatarka shine kasa takardar ta kara baki wanda zai juna wa mutane cewa takardar tayi gwagwarmay a rayuwa, to sai ka barbada garin kofee a kan takardar. Idan baka da garin to zaka iya yin amfani da garin neskofee. Shima nidan bazai samu ba, zaka iya fasa ganyen shayi akan takardar. Amma ka sani cewa zaka karkade ragowar garin da ba shiga cikin takardar ba.

11. A goge ragowar shayin. Idan ka gama matakan da aka ambata a sama, sai ka saka tawul domin goge ragowar shayin dake saman takardar. Ammafa ka tabbatar cewa ruwa bai taru akan farantin da takardar take ba. Hakan zaisa aikin ka yayi kyau sosai.

12. Sai abar takardar ta bushe. Idan ba sauri kake yi ba zaka iya barin takardar zuwa awanni ashirin da hudu (kwana daya) domin ta bushe. Sannan kuma kar a sakata a kasan rana, zaifi kyau idan zaa samu waje mai inuwa sannan kuma isaka tana busawa sosai.

13. A saka ta a oven. Idan sauri kake domin kayi amfani da takardar, zaka iya sakata a cikin oven domin tayi saurin bushewa. Amma a lura kar a saka mata wuta da yawa. Saboda haka, sai ayi amfani da zafi mafi karanci a jikin oven din domin busar da takardar. Yawancin oven suna zuwane da zafi mafi karanci a matsayin 93 degree celcius.

A gasa ta na mintuna kamar biyar. Idan ka zabi ka sakata a oven ne, to sai ka barta har zuwa mintuna biyar. Amma kuma ka dinga lura da ita a wannan lokacin kar ta kama da wuta. Amma kuma idan takardar tana da kauri, sai ka barta sama da mintuna biyar dana ambata a baya.

14. A goge saman takardar. Bayan an ciro ta daga cikin oven, yana da kyau ayi amfani da burushi mai laushi domin goge saman takardar. Amma hakan zaiyi amfani ne kawai idan ka sakawa takardar kofee ko kuma TUMERIC da aka ambata a  baya. Idan abaka ba burushi mai laushi, zaka iya amafani da tsumma mai lausho domin yin hakan.

15. Sai ka nannade takardar/cukurkuda ta idan kaga bata tsufa da yawa ba. Bayan ka nannade ta sai ka mikar da ita domin kaga ko ta tsufa yadda kake so. Bayan nan kuma sai kaje ayi maka laminashan din takardar domin kar ta yage ko lalace nan gaba.No comments:

Post a Comment