Thursday, 10 January 2019

Yadda Ake Amfani Da Lambobin Bankin Zenith Na 966


A wannan karnin da tura kudi, siyan kati, biyan kudin wuta da sauransu sukayi sauki. Zenith bank suma sun kawo nasu tsarin domin yin wadannan abubuwan dana ambata a baya ta hanyar amfani da wayarka.

Kafin kayi amfani da wannan lambobin ka sani  wasu abubuwan bazasuyi aiki ba sai akan layin da kayi regista da bankin. Sannan kuma wani abun sauki shine baka bukatar yanar gizo.

Idan kana son fara amfani da sai kayi regista ta hanyar danna *966*00#. Daga nan sai ka saka lambobin hudun karshe na katin cire kudinka (ATM Card). Daga nan zakaga sunanka da kuma inda zaka saka sabuwar  lambar tsaro. Daga nan zai bude maka wajen da zaka maimata lambar tsaron. Idan komai yayi dai-dai zasu turo maka sako dauke da yawan kudin cikin asusunka.

1. Domin  ka bude sabon asusun ajiya (New Account) da Zenith bank sai ka danna *966*0#.

2. Domin ka duba kudin da yake cikin asusun ka (Check balance) sai ka danna *966*00#

3. Domin siyan kati a lambarka (buy recharge for self) sai ka danna *966*KUDIN#. Misali Idan naira dari zaka saka sai ka danna *966*100#.
4. Domin siyan kati a wani layin (airtime for others) sai ka danna *966*KUDI*LAMBA#. Misali Idan zaka tura naira dari zuwa wata lamba sai ka danna *966*100*08065555555#.

5. Domin tura kudi zuwa wani asusun sai ka danna *966*KUDI*Lambar-Asusun#. Misali Idan zaka tura naira dubu zuwa wani asusun sai ka danna *966*1000*123456789#.

6. Domin hada lambar BVN zuwa account din sai ka danna *966*Lambar-BVN#.

7. Domin chanza lambar tsaro sai ka danna *966*60#.

8. Domin daina amfani da Banki ta waya sai ka danna *966*20*0#.

No comments:

Post a Comment