Thursday, 3 January 2019

Hanyoyi goma da zasu saka tsohuwar budurwarka ta dawo sonka
Sanin duk wani ma’abocin soyayya ne cewa, dole akwai damuwa da shiga qunci yayin ka samu rabuwa da abar qaunarka, to amma dole se ka jure na dan wani loqaci matuqar kana so ku koma soyayyar ku kamar yadda kuke a baya  ko ma sama da haka.

Shin ko kasan cewa……
A lokacin da masoyiyar ka tace zaman ku tare yazo qarshe, sannan ta fada maka maganganun da bai kamata ta fada maka ba, na bacin rai da cin mutunci. Yayin data koma gida ta nutsu, ta fara tinani, a wannan loqacin ne duk abinda ta fada zai fara dawo mata a cikin zuciyarta, zata dan fara nadamar wasu abubuwan data fada, zata dinga fada a zuciyarta cewa duk abinda kayi baka cancanci irin wannan zafafan kalamai ba.

A yayin da kai kuma zaka dinga tinanin cewa ba zaka ya rayuwa da kowa ba in ba da it aba, zaka rinqa jin cewa in kullun zagin ka zata dinga yi kana son kayarka a haka. Domin soyayyar gaskiya kake nuna mata, ko da ace wani zai dinga gaya ma cewar ka rabu da ita, ko da ka yadda dashi, daga baya sai kaji baka ji dadin shawarar daya baka ba.

Kusan kaso 80% na mutane haka suke I yayin da suka samu matsala tare da masoyansu.
BARI NA BAKU WANI SIRRI…..
Haqiqa tana tinanin baka cancanta ka zama masoyinta ba, shi yasa ta raba alaqar taku, wataqila tana ganin baka da wani abu da take so. Saboda haka ya zama dole a gareka ka tabbatar mata da cewa kai ma dan halak ne, ka nuna mata cewa ko ba ita zaka iya rayuwa, ka nuna mata cewa akwai mutane da yawa da suke sonka, kuma a shirye suke su baka loqacinsu da rayuwarsu baki daya.

Misali: kai ne kaje siyan riga se aka ce maka ai rigar nan Naira 100 ce, duk da kana son rigar se kaga tayi maka tsada, ka fasa siya kayi tafiyar ka, washe gari ka zo wucewa se kaga mutane sun cika a shagon da kaga rigar nan, ka tambaya se aka cema ai wannan rigar ce ake mata layi kuma kudinta naira 2000 ne. zakayi nadamar rashin siyan rigar nan ko bazaka yi ba? To haka muke so masoyiyar ka taji. Muna so ta gane cewa bawai masoya ka rasa ba da take wulaqanta ka, hakan zai temaka matuqa wajen dawowar ta.

In kabi wadannan hanyoyi, da ikon ubangiji se ta dawo gareka cikin gaggawa da:

1. Kayi tinani da karatun nutsuwa akan cewa soyayyar taku zata dore har gaban abada idan kayi qoqari kuka shirya, ko kuma matsalolin da aka dinga samu a baya sune zasu ci gaba da faruwa ba tare da an samu canji ba.

2.  Kada kayi tinanin cutar da kanka zai saka ku dawo, misali ka daina cin abinci, ko ka saka damuwa a zuciyar ka, ko kuma ka nemi ka kasha kanka. Domin hakan zai tabbatar mata da cewa kana so ka rayu saboda da ita.

3.  Kada ka kuskura a yayin da masoyiyar ka ta nuna maka tana so ku dawo ka nuna baka so, ka karbe ta hannu biyu-biyu Alaji.

4.  Kar kaje ka dinga fada wa mutane cewa kun yi fada, ko ta yaudare ka, ko wani abu makamancin irin wannan don hakan na janyo gaba mai tsanani tsakaninku.

5.  Kada ka dinga bi kana gayawa abokanka da yan’uwanka abubuwan da kayi mata loqacin da kuna tare don hakan zai janyo rashin yuwowar dawowarku har abada.

6.  Ka ci gaba da kyautata mata, ko ta daina daga wayarka kada kayi fishi, ka dan dinga tura mata saqonni ta hanyar text message a qalla sau 3 a sati.

7.  Ka dinga yawan tina mata loqatan da kukayi na farin ciki da jin dadi, saboda tino da abin da ya wuce na farin ciki ka iya sakawa taji tana so ku dawo.
8.  Ka duba abubuwan da yake sakata farin ciki, ka yawaita yinsu, usamman a inda zata dinga gani. Hakan zai saka ta karkato izuwa gareka.

9.  Wani loqaci dole ka dinga nuna mata cewa kana so ku dawo, amma ba ko yaushe ba. Saboda tasan cewa baka manta da soyayyar da yi a bay aba.

10.  Idan saqonnin da kake tura mata bata taba dawo maka da amsa ba, to shawara mafi sauki ka haqura da soyayyar nan, saboda ba soyayyarka a zuciyar ta ko kadan.

No comments:

Post a Comment