Sunday, 20 January 2019

Amfanin Miyar Kuka a Jikin dan Adam

                 

Mutane da yawa basa son kuka, ko ince miyar kuka a dunqule, na tabbatar rashin sanin amfanin ta ne a jiki yasa mutane basa sonta. Amma idan miyar kuka tasha kayan hadi ina tabbatar muku da cewa ba zaka gane kuka bace sai ka fara qoshi saboda dadin ta. Bazai yiwu mu kawo gaba daya amfanin kuka a jikin mutun ba, sai dai mu kawo wanda ya samu, saboda har yanzu ba’a gama gano wasu daga cikin amfanin nata ba.
Ga kadan daga cikin amfanin nata.

1. Kuka tana da amfani ba kadan ba wajan kawar da matsalolin gurbacewar ciki.

2. Ana amfani da kuka don maganin yunwa, a bangaran abinci, tana qara wa abinci qanshi da kuma dadi.

3. Shan kuka yana qara qarfin qashi, domin tana dauke da sinadarin nan mai suna calcium mai dimbin yawa.

4. Kuka tana maganin cutar cizon sauro wacce aka fi sani da malaria.

5. Amfanin kuka bai tsaya anan ba domin har maganin qarancin jini take a jikin bil-adama.

6. In kana musu ka tambayi likitanka zai gaya maka kuka tana maganin ciwon haqori.

7. Bugu da qari kuka tana taimakawa wajan taimakawa garkuwar jikin mutum domin kare shi daga cututtuka da dama.

8. Kuka tana taimakawa wajan yaqi da cutar nan mai suna tarin fuka (asthma)

No comments:

Post a Comment