Monday, 7 January 2019

Yadda zaki/ka gane masoyinka/ki suna son ku rabu.

Mutane da dama suna son su rabu da masoyansu saboda wani dalili wanda yake boyayye a zuciyoyinsu. To koma wanne irin dalili ne, akwai hanyoyin da zarar ka/kin fara ganin masoyiyar ka ko masoyinka ya fara nuna maka/ki su to ya kamata ka/ki ja baya , domin komai zai iya faruwa matuqar ba ka/ki yi hakan ba.

1. Zai/zata daina fada maka/ki wasu abubuwan da suka same ta/shi a kamar yanda ya/ta saba.

2. Lokacin da ya/ta ke ba ka/ki zai/zata rage shi sosai, uzururruka zasu yi yawa, dama abinda bai kamata ace uzuri bane.

3. Daa in kuna zaune har sai ya/ta ishe ka/ki da surutu, amma yanzu gaba daya bama ya/ta son yawan Magana.

4. Zaku dinga yawan fada na babu gaira babu dalili, abinda ma bai kamata ace kunyi fada ba sai ku fara fada a kansa.

5. Zai/zata fara nuna miki/maka cewa shi fa dama tin farko, akwai wasu halayenki/ka da baya/ta so, kawai dai ya/ta yi haquri ne ya/ta ga ko zaki/ka canza kuma ka/kin qi canzawa. Kuma ya/ta fuskanci har abada bazaki/canza suba.6. Babu ranar banza kullun se kunyi fada, kai kace a kanku aka saukar da yaqin duniya na biyu. Kuma fadan kullun babu wani kyakykyawan dalili.

7. Abokansa/kawayenta suna yawan zuga shi/ta akan ya/ta rabu da ke/kai, da zarar ka/kin ji haka ki/ka fara ja baya domin zai wuya a daure a haka.

8. Zai/zata daina yawan kiran ki/ka a waya, text message dinma ta/ya daina gaba daya, kuma in kin/ka yi qorafi zata/zai ce maka/miki ai abubuwa ne suka dan yi yawa kwana biyu.


No comments:

Post a Comment