Wednesday, 9 January 2019

Yadda zaki janyo hankalin saurayi ya fara sonki

     
Mata da yawa a wasu loqutan suna matuqar cutar kansu, saboda kunya, to amma haka ake so duk wata macen kwarai ta kasance. Ba anan gizo ke saqar ba, wasu matan suna kamuwa da soyayyar saurayi amma su rasa yadda zasuyi da rayuwarsu wajen gaya masa. Anan zamu baki abinda bature yake kira da ”tips” wato satar amsa, cikin sauqee ba tare da kin sha  wahala ba zaki shawo hankalinsa dan dole ya fara sonki.

1. Duk sa’ad da kika ganshi, ki yawaita murmushi, domin sakin fuska ko a gurin maqiyinka yana sawa ya sassauta maka wani loqaci. kuma da sirrin dake cikin murmushi ba kadan bane.

2. Idan kina da wani halin da mafiya yawancin maza basa so, to ya kamata kiyi kanki karatun ta nutsu ki canza wannan halin naki, koda kuwa baki da tabbacin  yana daya daga cikin mazan da basa son irin wannan aiki ko baya ciki.

3. Ki rinqa yawan fita ke kadai, ki rage yawo da qawayanki da yawa, koda ya zama dole sai kin fita da qawarki to ki zabi guda daya daga ciki kawai.

4. Karki sake ki fita aba tare da kinyi kwalliya ba, sai dai in kin san cewa kina daya daga cikin matan da ko busu yi kwalliya ba suna da kyau, matan da ake kira da natural beauty.
5. Ki rinqa yawan bari kuna hada ido da shi, domin hakan zai saka ya fara tinanin any aba wani abu a qasa, daga ina tabbatar miki da cewa sai ya kamu.

6. Idan yazo zai miki Magana, kada ki fara yin wasu abubuwan da kinsan ba halin ki bane, ki futo mai a yadda kike. Misali; wasu matan zasu ce zasu gyara muryar su, wasu kuma suce zasu ja aji. A ah, in kin san kina jan aji zaki iya yi, in kin san biki saba yi ba, to ki manta da hakan.

7. Ki maida hankali sosai yayin da yake Magana, saboda kar ya dauka ke daqiqiya ce, yayin da ya tambayeki kika kasa bada amsa.

8. Kar kiji kunyar gaya masa abinda kike so da abinda bakya so, dan daga nan ne zaku gane shin kun cancanci juna ko kuma zaman bazai yiwu ba.

9. Kar ki zama shashasha a gaban sa, idan kuna magana kar ki dinga nuna masa cewa ke doluwa ce, kawai saboda ki jawo hankalinsa. A'a hajiya, ki nuna masa cewa kin girma ya fahimci cewa ke ba yarinya bace, domin hakan zai saka ya kara yarda dake.

 10. Kada ki manta da tsaftar bakinki, domin in bakinki akwai matsala, ina tabbatar miki da cewa bazaku gama ba zai gudu, domin ba wanda zai iya zance da qazama

No comments:

Post a Comment