Thursday, 24 January 2019

Yadda matsalolin haila suke da rikice rikicen ta

                     
Jinin haila wani jini ne da yake fita daga al-aurar mace wanda ke nuna cewa mace zata iya daukar ciki. Kuma alama ce ta balagar ‘ya mace. Manyan malaman musulunci sunyi bayani cewa jinin haila abinci ne ga ‘da yayin da yake mahaifar uwarsa har zuwa loqacin da za’a haife shi, shi yasa idan muka duba zamuga cewa matan da suke dauke da ciki da yawansu basa fitar da jinni haila.

KALAR JINI HAILA

Kamar yadda malaman musulunci suka yi bayani, shi dai jinni haila kala uku ne, matsawar babu wani abu da ya cudanya dashi, wato ya kan canza kala idan ya hadu da wani abun. (1) launin fatsa-fatsa (2) launin qasa-qasa kamar ruwan daya lalace. (3) launin ja. Haka zalika idan mace na fama da lalurar rikicewar jinni to jinni haila yakan canza daga kalarsa ta asali izuwa baqi, kamar yadda yazo a hadisin fadimatu bint abi hubaiyyish.
SHEKARUN DA MACE KE FARA HAILA DA DAINAWA.

Mace da dama suna fara haila da zarar sun kai shekara 12, amma ana samun matan da suke farawa kafin su kai shekara goma sha biyun, hadisai da yawa sun yi bayani akan loqacin da mace take daina haila, wasu sun ce 55, wasu 60, wasu kuma 70, amma wadannan hadisai a zance mafi inganci basu inganta ta. Saboda haka mafi inganci da aka samu a cikin hadisai ingantattu shine shekara 50. Amma ba hakan yake nunawa cewa wasu basa wucewa ba, ana samun matan da suke wuce wadannan shekaru amma basu daina fitar dashi ba.

TSAWON KWANAKIN HAILA

Babu wani hadisi ingantacce da ya iyakance kwanakin haila, ko kuma kwanakin da za’a ce mace ta tsarkaka, kamar yadda Ibn Taimiyya, Ibnul Munzir, Ibnul qayyim al jauzi, Ash-shaukani da kuma sheik Sadiq Khan suka tabbatar. Gami da kuma aya cikin suratul baqara data qara tabbatar da hakan (quran 2;22).

Wasu malaman sunce hadisan da suka nuna cewa kwana uku ne  mafi qarancin kwanakin haila kuma mafi yawanci shine kwana 15, wadannan basu inganta ba. Hadisin da yayi maganar kwana 6 ko 7 , ya shafi wadda ke jinni cuta ne.

ABINDA AKA HARAMTAWA MACE MAI HAILA

Akwai abubuwa da yawa da aka hana mai haila ta aikata su. Malamai sun dace akan wasu, kuma sun samu sabani akan wasu.
1. Dawafi; kamar yadda aka samu muslim ya ruwaito; idan hailar tazo bayan anyi dawaful ifaadah, to ba zata jira daukewar ta ba don tayi dawaful wadaa. An dauke mata wannan dawafi.

2. Sallah da azumi: kamar yadda aka karbo daga Uwar muminai Nana Aisha R.A cewa manzon Allah s.a.w ya umarcesu da su rama azumi amma bai umarcesu da su rama sallah ba. Bukhari da muslim suka ruwaito.  To anan zamu ce mai haila dole zata rama azumin da ta sha yayin da take haila, amma bazata rama sallah ba.
3. Saduwa: yazo cikin suratul baqara, Allah s.w.a yace :”kuma suna tambayar ka game da haila? Kace: shi cuta ne. saboda haka ku nisanci mata a cikin wurin haila, kuma kada ku kusance su sai sun tsarki. To, idan sunyi wanka sai kuje musu daga inda Allah ya umarce ku. Lalle ne Allah yana son tuba, kuma yana son masu tsarkakewa”. (quran 2:222)       daga wannan ayar zamu fahimta cewa Allah yayi hani akan saduwa da mace mai haila har sai ta yi tsarki.

4. Saki: Allah madaukakin sarki ya fada mana cikin qurani mai girma:”  ya kai Annabi! Idan kun saki mata, sai ku sake su ga iddarsu, kuma ku qididdiga iddar”. (quran 65:1). Abinda ake nufi da saki ga idda shine; wato ya sake ta saki guda a cikin sauqin da bai shafe ta ba, ma’ana ta gama idda kuma bai sadu da ita ba.

5. Zama cikin masallaci: hadisan da suka zo akan cewa mace mai haila ba zata shiga masallaci ba basu inganta ba, wasu ma suka ce koda ba zama zatayi ba, bashi halatta ta shiga masallaci. Tare da cewa hakan ya saba wa ingantattun hadisai daga wajan; Nana Aisha da kuma Abu Hurairah.

6. Daukar alqur’ani:  malamai sun samu sabani kan hakan, wasu malaman ma haka suka ce ko karantawa baza tayi ba. Wasu kuma sunce zata iya daukar wani bangaran domin karantawa. In kuma hafiza ce to zata iya yin karatun ta tin daga suratul fatiha har nasi da k aba tare da ta dauka ba.

Zamu dakata anan. Sai kuma futowa ta gaba inn shaa Allah.
  

No comments:

Post a Comment