Wednesday, 30 January 2019

Yadda matsalolin haila suke da rikice rikicen ta 2

ABUBUWAN DA SUKA HALARTA GA MAI HAILA

Kabbara da Zikri: yana halatta ga mace mai haila tayi zikri, bismillah, hailala, haiqala, ko kuma kabbara. A wurin cin abinci, ko haka kurum domin samun lada, ko kuma karanta hadisi ko addu’a ko kuma karatun litattafan ilmi. Saboda abinda yazo a cikin sahihul bukhari da kuma sahihul muslim dama waninsu cewa manzon Allah s.a.w yana kwanciya akan cinyar nana Aisha R.A a loqacin tana haila kuma yana karatun al’qurani.

Zuwa wurin sallah: ya halatta ga mace mai haila taje wurin sallah ba tare da tayi sallar ba. Saboda zuwan hadisin manzon Allah s.a.w da aka karbo daga bakin ummu Atiyyah, tace: naji manzon Allah s.a.w yace: kubar matan da suka balaga, da matan da aka killace, da kuma matan da suke haila su fita. Ma’ana ai zuwa sallar iidi,domin su shaida yadda taron musulmai yake, amma mata masu haila su nisanci wajan sallar.” Au kama qalal rasool s.a.w.Aikin hajji: yana halatta ga mace ga haila ta tsaya arafa, ta yi kwanan mustalifa da minna, jifan shaidan da sauran ayyuka da akeyi a aikin hajji da umura, amma banda dawafi kamar yadda muka ambata a baya. Kenan idan haila ta samu mace bayan tayi dawafin farko zata iya qarasa ragowar ayyukanta amma banda dawafi bankwana. Saboda hadisin Abdullahi dan Abbas da yake cewa: manzon Allah s.a.w ya gaya wa mutane cewa abinda zasuyi na qarshe shine dawafi a dakin Allah, amma ya daukewa mace mai haila. Idan haila ta same ta kafin ta fara dawafi (dawaful ifadah), to sai tayi ragowar aiyukan idan ta samu tsarki sai ta je tayi dawafin. Allahu shine mafi sani. Idan taji tsoron kubucewar aikin hajjin a dalilin yin dawaful ifadah, to sai tayi qunzugu, tayi dawafinta, kuma dawafin yayi. Ibn taimiyyah ya rinjayar da wannan fahimtar.

Aure: ya halatta a daura wa mace aure a loqacin da take haila, amma fa mu sani baya halatta mijin nata ya kusance ta har sai tayi tsarki.

 Ya halatta aci abincin da mai haila tayi, da kuma cin abinci tare da ita. Saboda da zuwan hadisin nana Aisha r.a
                        
     ZARCEWAR JININ HAILA

Idan jinin haila yaqi tsayawa, ko mace taga tana haila sama da sau biyu a wata daya, ko kuma jini baya dadewa yake tsayawa misali kwana daya ko biyu sai taga ya tsaya, to wannan ya zama jinin cuta. Saboda haka abinda zatayi shine zata duba taga kwana nawa take haila kafin ta fara samun wannan matsalar, sai ta yi amfanin da wadannan kwanaki na baya. Kamar yadda yazo a hadisin ummu habiba: ta tambayi manzon Allah s.a.w akan jinni da yake zuba bayan ta gama haila har tsawon shekara bakwai: sai ya umarce ta da tayi wanka bayan kwanaki hailer ta data saba yi, ya qara da cewa daga jijiya jinni yake, saboda haka tana wanka a duk sallar da zatayi.”

Idan mace bata san kwanakin da take yin hailar taba, amma zata iya banbancewa tsakanin jinin al’ada da jinin cuta, zatayi amfanin da launin baqi mai kauri mai tsananin doyi a matsayin haila, shi kuma jinni cuta yana kasancewa ja mara kauri.
Idan kuma bazata iya banbancesu ba sai ta dauki kwana 6 ko 7 a matsayin kwanakin hailar ta bisa lura da kwanakin ta da tsarkinta keyi.Malamai sunyi maganganu da dama wajan yin salla da azumi mai haila. Idan ta fara jini koda gab da rana zata fadi ne a cikin azumi matuqar ranar bata fadi ba, bata da wannan azumin, idan kuma alama taji amma ba futowar jinni har rana ta fadi to azumin ta ya cika, idan loqacin sahur ya sameta tana haila bata da wannan azumi koda kuwa loqacin na fita tayi tsarki, amma idan tayi tsarki kafin hudowar alfijir to ko batayi wanka ba zata iya jin azumin ta. Game da sallah kuma malamai suka ce in dai har loqacin da tayi tsarki zata iya samun koda raka’a ne a cikin loqacin wannan sallar to sai ta rama wannan sallar. Manyan malaman mazhabobi guda 3(imam maliku, Ahmadu bin hambal da shafi’i) na ganin cewa idan jinin ya dauke kafin faduwar rana da kimanin raka’a 1, zatayi sallar azahar da la’asar, idan kafin fitowar alfijir ne zatayi magariba da kuma isha’i.

Malamai na ganin cewa ya halarta mace ta sha maganin da zai tsayar mata da al’adarta domin ta samu yin azumi gaba daya ko aikin hajji, in har mijinta ya yadda( ga masu aure), kuma ba wata matsala dangane da lafiyarta.
Idan ba ruwa yayin da mace ta tsarkaka to taimama ta wadatar kafin samuwar ruwan, kuma mijinta zai iya saduwa da ita a wannan yanayin. Haka zalika jinin cuta baya hana miji saduwa da matarsa.

Allah yasa mu dace. Ameen

No comments:

Post a Comment